Kwamitin Tsaro zai gana kan harin makamai masu guba a Syria

Ana sa ran Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai gana in an jima kadan domin tattauna zarge-zargen da ake yi cewa dakarun Syria sun yi amfani da makamai masu guba a lokacin da suka yi lugudan wuta a wani yanki dake wajen babban birnin kasar Damascus.
'Yan adawar Syria sun ce an kashe daruruwan mutane a lugudan wutar, wanda gamayyar 'yan adawa a Syria ta bayyana da cewa kisan kiyashi ne.
Sai dai kuma gwamnatin Syrian ta musanta zargin da ake wa dakarun ta na amfani da makamai masu guba.
Wani likita a Syria, Ghazwan Bwidany ya bayyana cewa da sanyin safiyar yau ne suna bacci sojojin Assad suka harba rokoki shida a kan garuruwa uku da ke gabashin Ghouta.
Jim kadan bayan faruwar hakan, sai daruruwan mutane suka yi ta tururuwa zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da alamar rauni a jikinsu.
An dai kai wannan hari ne a lokacin da wata tawaga ta duniya ta isa Syriar don binciken a kan wasu hare-haren makamai masu guba da aka kai a baya, da kuma binciken ko wane bangare ne ya kai harin.







