APC ta mika shugabannin riko ga hukumar zaben Nijeriya

Malam Ibrahim Shekarau, kusa a APC
Bayanan hoto, Malam Ibrahim Shekarau, kusa a APC

Kwamitin hadaka na jam'iyyun adawa dake kokarin dunkulewa wuri daya domin kafa jam'iyyar APC a Nijeriya, ya bayyana sunayen mutane tara, a matsayin shugabannin jam'iyyar na rikon kwarya.

Kwamitin hadakar, karkashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau, ya ce tuni ya mika sunayen mutanen, da suka hada da shugabanin jam'iyyun uku; Cif Bisi Akande na ACN, da Dr Ogbonnaya Onu na ANPP, da kuma Cif Tony Momoh na CPC , da sakatarori da kuma masu rike da mukaman ma'aji na jam'iyyun uku ga hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Dunkulewar manyan jam'iyyun adawar uku domin kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriyar, na ci gaba da janyo sharhi iri daban daban.

Wasu na ganin ta haka ne kawai zasi iya hada karfi da karfi su kayar da PDP wadda ke cewa zata mulki kasar nan da shekaru hamsin masu zuwa.

Sai dai akwai wadanda keda ra'ayin cewa bambancin ra'ayin dake tsakanin kusoshin jam'iyyun , sun sa da wuya tafiyar ta dore.

Su dai sun ce sun daura damarar ba marada kunya.