Ana taro kan sauyin yanayi

A ranar Litinin ne ake fara taron Majalisar Dinkin Duniya don shata manufofin tunkarar sauyin yanayi a birnin Bonn na kasar Jamus.
Manufar taron ita ce dorawa daga inda aka kwana a yarjejeniyoyin da aka cimma yayin taron da aka yi a kan sauyin yanayin a birnin Doha na kasar Qatar.
Kusan kasashe dari biyu ne suka amince a tsaiwata yarjejeniyar Kyoto a kan yaki da dumamar yanayi zuwa 2020 a taron da aka yi a kwanakin baya a birnin na Doha.
Sauyin yanayi da illolin da yake haifarwa a kan muhalli dai babbar barazana ce ga rayuwar dan-Adam da ci gabansa.







