Arsenal na son Guehi, Madrid za ta sayar da Rudiger

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta shiga hammaya kan ɗanwasan baya na Ingila mai shekara 25 na Crystal Palace Marc Guehi. (Mirror)
Sai dai Manchester City tana da ƙwarin guiwar za ta mallaki Guehi nan da kwanaki masu zuwa domin shan gaban Livepool. (Star)
Tottenham ta cimma yarjejeniya da ɗanwasan baya na Brazil da Santos Souza. (Fabrizio Romano)
Wolves na son riƙe matashin ɗanwasanta na Ingila Mateus Mane inda ta nace cewa ba na sayarwa ba ne. (Mail)
Ɗanwasan gaba na Masar Omar Marmoush, mai shekara 26, ba ya son barin Manchester City a Janairu. (Florian Plettenberg)
Real Madrid ta matsa kan ɗanwasan baya na Borussia Dortmund da Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 26, yayin da ɗanwasan baya na Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 27, ake sa ran zai sabunta kwangilarshi a Bayern Munich. (Bild - subscription required)
Manchester City na son ɗauko ɗanwasan Brentford da Italiya mai shekara 21 Michael Kayode. (Caughtoffside)
Real Madrid na son sayar da ɗanwasan bayanta na Jamus Antonio Rudiger a Janairu kan fam miliyan 9 inda Chelsea da Paris St-Germain suka nuna buƙatar ɗanwasan wanda kwangilar shi a Bernabeu za ta kawo karshe a bazara. (Fichajes - in Spanish)
Aston Villa ta amince kan yarjejeniyar fam miliyan 10 kan matashin ɗanwasan gaba na Metz da Luxembourg Brian Madjo. (Fabrizio Romano)











