An sace wasu Faransawa bakwai a Kamaru

An sace wani gungun Faransawa 7 a arewacin Kamaru kusa da kan iyaka da Najeriya.
Shugaba Francois Hollande ya ce dukkanin mutanen 7 yan gida daya ne, hade da yara 4.
Ya ce wata kungiyar dake Najeriya ce da hukumomin Faransa suka sani ta kame su.
A ranar lahadi an sace baki 'yan kasashen waje 7 a Najeriya mai makwabtaka, a wani harin da aka dora alhakinsa kan kungiyar masu tsatstsauran kishin Islama ta Najeriya.
A watan da ya wuce Faransa ta aike da dakarunta zuwa Mali domin taimakawa ga fatattakar yan tawaye masu kishin Islama a can.
Akalla dai Faransawa 8 ne kungiyoyin masu kishin Islama ke rike da su a yankin Sahel.
Jami'an tsaro a Kamaru sun ce sun yi amanna cewa, mutanen na komowa ne daga wajen shakatawa na Waza, inda 'yan kasashen waje ke zuwa yawon bude ido.
An ambato ofisihin jakadancin Faransa a Yaounde na cewa, wasu yan bindiga ne a kan babura suka kame mutanen, inda suka nufi Najeriya da su.
france











