Gwamnonin adawa a Najeriya na goyon bayan hadewa

A Najeriya, gwamnonin jihohi goma da suka fito daga jam'iyyun adawa daban-daban sun amince su dunkule waje guda don samar da jam'iyyar da za ta kalubalanci jam'iyyar PDP mai mulki a zabukan da ke tafe.
Gwamnonin dai sun bayyana hakan a wani taro da suka gudanar a Lagos.
Sun bayyana cewa yunkurin nasu yana da matukar muhimmanci saboda a ceto kasar daga matsalolin da take ciki, wadanda jami'iyar PDP ta kasa magancewa.
Gwamnonin sun kara da cewa sun gudanar da taron ne domin su karfafa gwiwar kwamatocin da jam'iyun suka kafa don duba yiwuwar hadewar su.
A shekarar 2011 dai, jam'iyun ACN da CPC sun yi kokarin tsayar da dan takarar da zai fuskanci jam'iyar PDP amma lamarin ya ci tura.







