An gayyaci Shugaban 'yan adawar Syria zuwa Rasha

An gayyaci shugaban hadin gwiwar manyan kungiyoyin adawa a Siriya Ahmed Moaz al Khatib zuwa Moscow a lokacin tattaunawar da ya yi ta farko kai tsaye da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov.
Mutanen biyu sun gana ne a daura da taron kasashen duniya kan al'amuran tsaro a birnin Munch na kasar Jamus.
Wakilin BBC yace akwai alamar Rasha ta dan sassauto duk da cewa ra'ayi ya banbanta tsakanin Moscow da sauran wakilan kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a game da yadda za'a magance rikicin Siriya.
Ana dai ci gaba da samun rahotannin asarar rayuka a wannan rikici na Syria.







