An gano gawawwaki fiye da 50 a Syria

Masu fafutuka na 'yan adawa a Syria sun ce an gaano wasu gawarwaki fiye da hamsin na mazaje a cikin wani kogi dake Aleppo birni mafi girma a kasar.
'Yan adawan sun ce galibin mutanen an harbe su ne a ka, kuma da dama daga cikinsu an daure hannayensu.
Wakilin BBC ya ce wani hoton bidiyo da ba shi da kyaun gani, wanda aka wallafa a shafin Intanat, ya nuna gawaki da dama da tabo a jikinsu kusa da kogin Queig.
Masu fafituka sun yi imanin cewa an yiwa mutanen kisan gilla ne, bayan da sojojin gwamnati suka kama su.
An gano gawakin ne dai a yankin Bustan al Qasr na birnin Aleppo, wanda sojoji gwamnati da 'yan adawa suka yi ta kokarin kamawa, tun bayan da suka fara gwabza fada a cikin watan Yuli.







