'Ana ganawa fursunoni azaba a Afghanistan'

Majalisar dinkin duniya ta ce har yanzu ana ci gaba da da azabtar da fursunoni a gidajen yarin Afghanistan, sama da shekara guda bayan an fallasa irin wannan cin zarafi da ake yi.
Jami'an Majalisar masu bincike sun bada bayani kan irin wannan azabtarwa a ofisoshin 'yan sanda shidda, da ma wasu ciki har da wasu na hukumar leken asirin Afghanistan.
Daga cikin mutane sama da dari shidda da suka hada da fursunonin da ake tsare da su da wadanda aka saki da aka tambaya sama da rabinsu sun ce an gallaza masu ta hanyar duka, ko dodana masu wayar wutar lantarki, ko kuma ta hanyar lalata.
Gwamnatin Afghanistan dai ta ce akwai karin gishiri a zargin.







