Najeriya: Kaduna ta tallafawa 'yan gudun hijira

Alhaji Mukhtar Ramalan Yero
Bayanan hoto, Gwamnan Jihar Kaduna a arewacin Najeriya, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta bukaci 'yan gudun hijira a jihar, waɗanda har yanzu ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira da su yi hakuri da abubuwan da suka faru bayan zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2011, su barwa Allah komai.

Mutanen dai suna wurin ne tun watan Afrilun shekarar ta 2011 bayan baro Zonkwa a kudancin Jihar ta Kaduna, inda aka karkashe da dama daga cikinsu aka kuma ƙona gidajensu.

A wani bikin bayar da tallafin kuɗaɗe ga wadanda suka yi asarar gidaje da wuraren ibada yayin rikicin, gwamnatin ta buƙaci waɗanda suka bar gidajensu tun bayan rikicin kamar shekaru biyu baya ke nan, da su koma don ci gaba da zama, tunda kura ta lafa.

Gwamnan Jihar ta Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, ya shaidawa BBC cewa abin da gwamnatin ta baiwa 'yan gudun hijirar tallafi ne ba diyya ba, "domin gwamnati ba za ta iya biyan diyya ba".

Ya kuma kara da cewa, "A yi hakuri da juna, a yafe wa juna, domin a zo a sake sabon zama kuma a zauna lafiya da 'yan uwa".