Ramalan Yero sabon gwamnan Kaduna

A yau aka rantsar da sabon gwamna a jahar Kaduna bayan rasuwar gwamnan jahar Patrick Ibrahim Yakowa a wani hadarin jirgin sama a jahar Bayelsa.
A jiya ne dai wani jirgin saman soji mai saukar ungulu dake dauke da Mr Yakowa da tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro Janar Andrew Azazi ya fadi a kan hanyarsa ta zuwa birnin Patakwal.
Inda baki dayan mutane shidan dake cikin jirgin suka rasa rayukansu.
Tuni kuma shugaban Goodluck Jonathan na Najeriyar ya bada umurni da a gudanar da cikakken bicike kan musabbabin hadarin jirgin.
Wannan umarnin na shugaba Goodluck din dai na kunshe ne a cikin sanarwar ta'aziyyar wadanda hadarin jirgin ya rutsa da su ne inda ya ce rashin nasu gagarumar asara ce ga kasar baki daya.
Mutumin da aka rantsar a matsayin sabon gwamnan jahar ta Kaduna dai shi ne mataimakin tsohon gwamnan Alh Muktar Ramalan Yero, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.






