Mutum-mutumin da ya kafa tarihi

Wani mutum-mutumin na kamfanin Liquid Robotics ya kafa tarihia duniya.
Mutum-mutumin ya shafe mil 10,000 daga birnin San Francisco na Amurka zuwa Australia ba tare da an tallafa masa ba.
Ya dai shafe sama da shekara guda kafin ya isa can, inda ya rinka tattara bayanai kan yanayin tekun Pacific.
Kamfanin da ya mallake shi Liquid Robotics, na da wasu mutum-mutumin guda uku a teku, duk da cewa daya daga cikinsu ya koma Hawaii saboda matsalar da ya samu.
Sabon shirin yara kanana
Manufar dai na da aniyar shawo kan matsalar lalata da kananan yara a internet.
A bangare guda kuma, kamfanin Amazon na shirin kaddamar da wani shiri na musamman domin yara kanana.
Shirin wanda zai samar da fina-finai da litattafai da wakoki ba adadi daga dala 3 zuwa 10 a wata.
Za a fara kaddamar da shirin ne a Arewacin Amurka - da kuma manhaja a kwamfiyutar hannu ta Amazon Kindle Fire.











