'Yan adawar Masar sun ketara shinge

Masu zanga-zangar adawar a Masar sun ketara wani shinge da sojoji su ka kafa masu don hana su kaiwa ga fadar Shugaban kasa a birnin Alkahira.
Dubban masu fafutuka sun hallara a kan hanyar zuwa fadar Shugaban ƙasar don neman a soke ƙuri'ar raba gardamar da za a yi kan tsarin mulki.
Firayim Ministan Masar, Hisham Qandil ya buƙaci dukkanin ƙusoshin siyasar ƙasar su shiga cikin wata tattaunawar ƙasa a ranar Asabar.
To amma tuni shugabannin 'yan adawar su ka yi watsi da irin wannan kira da Shugaba Morsi ya yi.
A wani lamarin kuma, hukumar zabe ta kasar ta dakatar da kuri'ar raba-gardamar da aka shirya gudanarwa ranar Asabar ga 'yan kasar Masar da ke zaune a kasashen waje.







