Dalilin da ya sa kungiyar ma'aikatan layin dogo za su yi yajin aiki

Ma'aikatan layin dogo na Najeriya za su yi yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba zuwa 20 ga Nuwamba.
Babban sakataren kungiyar ma'aikatan jiragen kasa ta Najeriya (NUR), Kwamared Segun Esan, ya tabbatar da haka.
Bayanai sun nuna cewa kungiyar ta sanar da mahukunta batun yajin aikin.
A baya dai kungiyar masu aikin jiragen kasa ta Najeriya NUR da 'yar uwarta, kungiyar manyan ma'aikatan hukumar sun bai wa gwamnatin tarayya da hukumar kula da jiragen kasa ta kasar wa'adin makonni uku domin biya musu bukatunsu da suka hada da karin albashi da alawus- alawus.
Sauran bukatun sun hada da inshorar lafiya da biyan alawus -alawus na ma'aikatan da suka samu karin girma tun daga 2018 zuwa yanzu.
Kungiyoyin sun ce za su ci gaba da fafutukar ganin cewa an inganta musu albashi saboda a bayyane take cewa tsarin albashin ma'aikatan jirgin kasa shi ne mafi karanci a kasar.
Gwamnatin Najeriya ta amince da gina layin dogo da zai haɗe biranen da ke gabar teku.
Sun kuma ce hatta Ministan Sufuri ya taba magana a kan halin da suke ciki idan aka kwatanta su da sauran takwarorinsu.
"Mai girma Ministan Sufuri ya taba yarda cewa ma'aikatan jirgin kasa na Najeriya cikin sauki za a iya gane su a cikin jama'a ta hanyar kamanni da suturarsu abin da ke nuna matukar rashin dacewar albashin da ake biya a kamfanin," In ji kungiyoyin
Kungiyoyin sun kuma kara da cewa: "Abin ya ba mu mamaki matuka yadda gwamnatin tarayya ke kashe biliyoyin daloli wajen gina ababen more rayuwa na sufurin jiragen kasa da sauya tsarin zuwa tsarin layin dogo na zamani amma babu wani tasiri ko inganta jin dadi da walwalar ma'aikata ta fuskar karin albashi.
"Muna mamakin har yaushe mai girma Ministan Sufuri zai ci gaba da gujewa ma'aikatan layin dogo da sanin ya kamata wajen samun ingantaccen albashi ga ma'aikatan layin dogo na Najeriya. Muna mamakin ko yaushe za mu jira kafin mu samu amincewar bukatarmu ta inganta albashi kamar yadda aka kara wa ma'aikatan Hukumar Kula da katin Shaida ta Kasa (NIMC) a baya baya nan.











