An dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya saboda tsaro
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, ta ce ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a ƙasar saboda tsaro.
NRC ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet a ranar Alhamis da rana.
Hakan na zuwa ne bayan da aka kai wa wasu jiragen ƙasa na hanyar Abuja zuwa Kaduna hari har sau biyu a jere.
Harin farko ya faru ne a ranar Laraba da yamma kan jirgin da ke tafiya Kaduna daga Abuja, sai kuma hari na biyu da ya faru ranar Alhamis da safe a kan jirgi mai tafiya Kaduna daga Abuja.
Wasu da lamarin ya rutsa da su a cikin jirgin sun ce harin ya jawo lalacewar layin dogon da jirgin ke bi.
Sanata Shehu Sani wanda ke cikin fasinjojin jirgin kasan ya ce "a ranar Alhamis da safe an kai hari kan jirgin kasa, sannan da yammacin a ranar Laraba jirgin ya taka nakiya, sannan aka buɗe masa wuta a daidai saitin da direba yake da kuma tankin jirgin".
"Ina cikin jirgin da safiyar nan a lokacin da jirginmu ya bi ta kan nakiya ta tashi, Ikon Allah ne kawai ya sa muka tsira," in ji tsohon sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya.

Asalin hoton, NRC
Ga wasu hotuna da BBC Hausa ta samu na jirgin bayan kai masa harin.

Asalin hoton, Others

Asalin hoton, Others
Me ya faru?
Tun da safiyar Alhamis wani tsohon Sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa an kai wa wasu jiragen ƙasa da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja babban birnin Najeriya hare-hare har biyu.
Ya ce an kai hari kan jirgin yamma na ranar Laraba inda jirgin ya taka nakiya, sannan aka buɗe masa wuta a daidai saitin da direba yake da kuma tankin jirgin.
Ya kuma ƙara da cewa an sake kai hari kan wani jirgin na safiyar Alhamis da shi sanatan ke ciki inda ya taka nakiya ta fashe har ta lalata hanyar jirgin.
"Ina cikin jirgin da safiyar nan a lokacin da jirginmu ya bi ta kan nakiya ta tashi.
"Ikon Allah ne kawai ya sa muka tsira," kamar yadda Sanata Sani ya wallafa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Hari ne ko matsala ce daga jirgin?
Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC ta tabbatar da cewa hari ne aka kai ta hanyar dasa abin fashewa kan titin jirgin.
Hukumomin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin Rijana da Dutse, kuma harin ya jawo lalacewar layin dogon da jirgin ke bi.
Sai dai wani da ke cikin jirgin ya ce bisa ga abin da suka ji kamar matsala ce daga kan jirgin.
"Mun ji warin mai a jirgin - ba za mu iya cewa jirgin ya taka nakiya ba"
Ya ce suna cikin tafiya sai suka ji ƙarar fashewar wani abu kamar bom a kan jirgin. "Jirgin ya tsaya, wutar jirgin ta mutu kuma AC ya daina aiki. "
"Mun zata matsalar ce da za a gyara a cikin karamin lokaci amma haka muka shafe fiye da awa hudu ba labarin abin da ke faruwa," in ji shi.
Ya ce sai can wuraren 12 na dare aka kawo wani kan jirgi daga Abuja da aka hada ya ja jirgin zuwa Kaduna.
A cewarsa, "Jirgin yana yi yana tsayawa kuma tafiyar da ba ta wuce minti 30 ba amma mun yi awa biyu kafin muka isa Kaduna wuraren karfe biyu na dare kowa ya tafi gida."
Halin da fasinja suka shiga
Wani da ke cikin jirgin ya shaida wa BBC cewa irin mawuyacin halin da fasinjan jirgin suka shiga inda ya ce sun shafe tsawon awa hudu cikin jirgin ba su san makomarsu ba.
Ya ce fasinja sun shiga cikin mawuyacin hali. "Kowa sai addu'a yake wasu har ba su son jin ana magana idan ba addu'a ba."
Ya ƙara da cewa saboda mawuyacin halin da aka shiga har ruwan bayi wasu suka koma suna sha saboda tsananin ƙishin ruwa.
Ya ce makewayin jirgin duk ya lalace saboda tsawon lokacin da aka kwashe a cikin jirgin sakamakon halin da fasinja suka shiga
"An kara kudin lemu daga naira 300 ya koma 500," in ji shi












