China ta haramta wa BBC watsa labarai a ƙasarta kan rahotannin musguna wa Musulman Uighur

BBC
Bayanan hoto, BBC ta bayyana takaicinta dagane da wannan mataki

Ƙasar China ta haramta wa BBC watsa labarai a kasarta, a cewar wata sanarwa da hukumar kula da kafafen watsa labarai ta ƙasar ta fitar ranar Alhamis

Ta soki BBC kan rahotontannin da take bayarwa da suka shafi cutar korona, da kuma muzguna wa musulmai 'yan kabilar Uighur marasa rinjaye.

BBC ta bayyana takaicinta dagane da wannan mataki.

Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumar kula da kafafen watsa labaran Birtaniya ta haramtawa kafar watsa labaran China ta CGTN watsa shirye shirye a kasar bayan gano cewa ta samu lasisinta ne ta haramtacciyar hanya.

An kuma same ta da keta dokokin watsa labarai na Birtaniya a bara, sakamakon sanya jawabin amsa laifi na karya, da wani dan kasar Peter Humphrey ya yi.

Mataimakin shugaban hukumar kula da watsa labarai ta China

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban hukumar kula da watsa labarai ta China

A hukuncin da ta yanke, hukumar kula da shirya fina finai da talabijin da rediyo ta Chinan, ta ce rahotannin da BBC ke yadawa sun yi matukar saba doka.

A don haka ne ta ce baza a amince da bukatar BBC ta ci gaba da aiki a kasar ta tsawon shekara guda ba.

Cikin wata sanarwa da BBC fitar ta ce : 'Muna takaicin yadda mahukuntan China suka yanke shawarar daukar wannan matakin. BBC ita ce kafar watsa labarai ta duniya da aka fi yarda da ita, kuma tana bayar da rahotanni kan labarai daga ko'ina a duniya bisa adalci, ba tare da nuna bambanci ko tsoro ko wata fargaba ba. "

Tashar Talabijin ta BBC World News dake samun kudi ta hanyar kasuwanci na watsa shirye shiryenta a duniya cikin harshen Turanci. Amma a China an iyakance ta, inda ake iya kallonta a otal-otal na kasa da kasa da kuma wasu tashoshin jakadanci kadai, abin da ke nufin cewa yawancin yan kasar a yanzu ba za su samu damar kallonta ba.

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniyya Dominic Raab ya kira matakin a matsayin "danne hakkin 'yan jarida da ba za a amince da shi ba".

BBC
Bayanan hoto, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniyya Dominic Raab ya kira matakin a matsayin "danne hakkin 'yan jarida da ba za a amince da shi ba"

Ita ma ma'aikatar Harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai da matakin, da ta kira a matsayin wani bangare na kokarin murƙushe kafofin watsa labarai a China.

Dangantaka tsakanin China da Burtaniya ta kara tabarbarewa a cikin 'yan watannin nan, musamman game da Hong Kong, inda Beijing ta gabatar da sabuwar dokar tsaro mai cike da cece-kuce.

A watan Janairu ne Birtaniya ta gabatar da wata sabuwar biza wacce ta bai wa mazauna Hong Kong fiye da miliyan 5 'yancin zama a kasar, sannan daga karshe su zama' yan kasa saboda ta yi imanin cewa China na tauye hakki da 'yancin yankin.

Sannan a cikin shekaru biyun da suka gabata China ta kan toshe ko kuma hana watsa labaran kasashen waje har ma ta kori wasu 'yan jaridar Amurka su uku a shekarar 2020.

Dama tuni aka dakatar da manhajar BBC da shafinta na Internet a kasar.

Tonon sililin da BBC ta yi

Google
Bayanan hoto, Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam dai sun ce kusan Musulman Uighur Miliyan daya ne ake tsare da su a sansanoni daban daban a kasar

A watan Fabrairu ne BBC ta samu muhimman shaidu da ke bayyana yadda ake yi wa mata fyade da azabtarwa a sansanonin killace Musulmai ƴan ƙabilar Uighur.

Matan, wadanda suka ce an tsare su a sansanin tsawon watanni, sun ce ana azabtar da su da ƙarafan laturoni.

Sun kuma bayyana wani abin da ya faru lokacin da aka tilasta wa kimanin fursunoni 100 kallon wata budurwa da jami'an tsaro suka yi wa fyaɗe a gabansu.

A cikin wata sanarwa, gwamnatin China ta ce ta duƙufa wajen kare 'yancin mata.

Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam dai sun ce kusan Musulman Uighur Miliyan daya ne ake tsare da su a sansanoni daban daban a kasar.

Ita dai China a kullum tana musanta zargin da ake yi mata na gallaza wa Musulman, inda take cewa tana ilmantar da su ne a wasu sansanoni na koyar da sana'o'in hannu domin kaucewa samun masu kaifin kishin Islama a ciikinsu.