Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni da bayanai dangane da mahimmman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 09/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjbir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. FIFA ta ce za ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48

    Hukumar Ƙwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce za ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta mata daga tawagogi 32 zuwa 48.

    Sabon tsarin zai fara aiki ne daga gasar 2031, wadda Amurka ce kawai ke neman ɗaukar nauyinta.

    Tuni dai FIFA ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta maza da za a yi nan gaba, zuwa wannan adadi.

    FIFA ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yadda gasar ke ci gaba da samun karɓuwa da farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a duniya.

    Masu suka sun zargi hukumar da fifita kuɗin da za ta samau fiye da la'akari da yawan wasanni da ƴan wasa za su fuskanta.

  3. Makiyaya daga ƙetare ne ke da alhakin mafi yawan kashe-kashen Najeriya - Sojoji

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta alaƙanta hare-haren baya-bayan nan da aka samu a jihohin Benue da Plateau da wasu sassan ƙasar da makiyaya daga ƙasashen waje, waɗanda rahotonni suka ce sun shiga ƙasar ne daga kan iyakokin ƙasar da ke buɗe.

    Yayin da yake jawabi ga taron manema a Abuja, Daraktan yaɗa labaran shalkwatar, Manjo Janar Markus Kangye ya amince cewa akwai hannu wasu ƴan Najeriya a hare-hare, amma ya ce mafi yawan kashe-kashen da ake samu ƴan ƙasashen waje ne ke aiwatar da su.

    “Ku sani cewa mafi yawan tashe-tashen hankulan da ke haddasa kashe-kashen da kuke ji a wasu sassan ƙasar nan, ƴan ƙasashen waje ne ke aiwatar da su,” in ji Manjo Janar Kangye.

    Manjo Janar Kangye, ya ce idan aka saurarin harsunan da maharan ke magana da su da kamanninsu za a tabbatar da cewa ba ƴan Najeriya ba ne.

    “Idan ka ji yadda suke magana, za ka tabbatar cewa ba ƴan ƙasarmu ba ne. Alal misali Hausar da ake yi a Najeriya ta bambanta da wadda ake yi a Mali ko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko Ghana,'' in ji Kangye.

    Ya ƙara da cewa, yadda suke magana da siffofinsu zai ƙara tababtar da cewa ƴan ƙasashen waje ne.

    Kakakin shalkwatar ya dage cewa “dole ne kowa ya bayar da gudunmowa a matsayin ƙasa guda wajen magance matsalar''.

  4. Kotun Amurka ta bayar da belin sakin ƴar Turkiyya da ta soki jami'arta kan yaƙin Gaza

    Alƙalan tarayya a Amurka sun bayar da belin wata ɗalibar jami'ar Tufts da wasu jami'ai suka kama fuskokinsu a rufe a lokacin da take tattaki a kusa da gidanta.

    An tsare Rumeysa Ozturk bayan ta yi wani rubutu game da ra'ayinta, inda ta soki martanin jami'ar Tufts kan yaƙin Isra'ila da Gaza.

    Lauyoyinta sun ce kamunta da aka yi cikin watan Maris ya saɓa ƙa'ida, inda kuma wasu ke ganin bai kamata a hukunta ƴar ƙasar Turkiyyan saboda amfani da ƴancinta na faɗin albarkacin baki.

  5. Amurka da Iran za su yi zama na huɗu kan shirin nukiliyar Iran a Oman

    Iran da Amurka za su yi zama na hudu a ƙasar Oman, a ranar Lahadin nan, domin tattauna shirin Nukiliyan Iran ɗin.

    Wani jami'in Amurka ya ce wakilin shugaba Trump na musamman, Steve Witkoff zai halarci zaman, yayin da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi zai wakilci ƙasarsa.

    Kwana guda kafin tattaunawar kuma, Mr Araqchi zai ziyarci Saudiyya da kuma Qatar, duk dai a game da batun.

    A zangon farko na mulkinsa ne shugaba Trump ya fitar da Amurka daga tattaunawar ƙasashen duniya mai ƙoƙarin sanya ido kan shirin Iran na mallakar makaman Nukiliya.

  6. Samun jam'iyyu barkatai na dagula tafiyar da gwamnati - Ganduje

    Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce samun jam'iyyu barkatai na dagula tafiyar da gwamnnati a tsarin dimokraɗiyya.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasar ranar Juma'a jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu tare da wasu ƴan majalisa da suka koma APC, Abdullahi Ganduje, ya ce idan duka jam'iyyun siyasar ƙasar za su narke su koma APC, suna maraba da hakan.

    ''Yanzu idan ka duba ƙasar China tsarin jam'iyya guda suke bi, amma yau ƙasar China jagora ce a duniya wajen samar da ci gaban al'ummarsu''.

    Ganduje ya ce idan ƴan Najeriya suka buƙaci komawa tsarin jam'iyyar guda, ba wanda zai yi faɗa da hakan.

    • Mece ce makomar manyan jam'iyyun adawa a Najeriya?
    • Me ke faruwa a jam'iyyar NNPP a jihar Kano?
  7. Hare-hare na ƙara munana a yankin Kashmir

    An ji ƙarar fashewar abubuwa da na ƙararrawar ankararwa da baƙin hayaƙi a yankin Kashmir da ake taƙaddama a kansa da kuma kewayensa, yayin da Indiya da Pakistan suka zafafa hare-hare kan juna.

    Ana ruwan hare-hare a jihar Junjab da ke Indiya a wani abu da Indiya ke gani a matsayin ƙaruwar tashin hankali.

    Sojojin Pakistan sun ce Indiya za ta ɗanɗana kuɗarta bayan ɓarnar da hare-harenta suka yi a Pakistan.

    Wakilin BBC a Islamabad ya ce Pakistan na bayyana damuwa kan taɓarɓarewar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    A ranar Laraba Indiya ta kai jerin hare-hare a wani abu da ta bayyana da martani kan zargin Pakistan da hannun a kisan wasu Indiyawa ƴan yawon buɗe idanu a yankin Kashmir a watan da ya gabata.

  8. 'Sanatocin PDP uku daga jihar Kebbi za su koma APC'

    Ƴanmajalisar Dattawan Najeriya uku na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi za su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya tabbatar.

    Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne ga manema labarai, jim kaɗan bayan ganawar sanatocin da Shugaba Tinubu a fadarsa da ke Villa.

    ''Sanatocin jam'iyyar PDP daga jihar Kebbi a yau sun tabbatar wa shugaban ƙasa cewa sun fice daga jam'iyyarsu ta PDP tare da dawo jam'iyarmu ta APC'', in ji Ganduje.

    Abdullahi Ganduje ya ce sanatocin uku za su bayyana wa majalisar dattawa matsayar tasu a mako mai zuwa kamar yadda kundin tsarin ƙasar ya tanadar.

    Sanatocin uku sun haɗa da Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi da kuma Sanata Garba Maidoki.

    A baya-bayan nan batun sauya sheƙa tsakanin manyan ƴansiyasa na ci gaba da ɗaukar hankali a ƙasar, bayan da wasu jiga-jigan jam'iyun hamayya ke komawa APC mai mulki.

    Ko a makonnin baya ma gwamnan jihar Delta da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa - wanda shi ne ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 - suka sanar da komawa APC.

  9. JAMB ta fitar da sakamakon jararbawar 2025

    Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar wannan shekarar da aka gudanar makonnin da suka gabata.

    Rajistaran hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka a shalkwatar hukumar a lokacin ƙaddamar da fitar da sakamakon.

    Sai dai hukumar ta ta riƙe sakamakon ɗalibai 39,834, waɗanda ta ce za ta yi bincike a kansu bisa zargin satar jarrabawam sannan kuma ana zargin kusan ɗalibai 80 da laifukan da suka shafi jarrabawa, inda jihar Anambra ke kan gaba.

    Hukumar ta kuma bayyana cewa daga cikin ɗalibai 2,030,862 da suka yi rajistar jarrabawar, 71,705 ba su samu damar rubuta jarrabawar ba.

  10. Ana fuskantar matsananciyar yunwa a tsakiya da yammacin Afirka - MDD

    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFP ya ce miliyoyin al'ummar tsakiya da yammacin Afirka ne ke fuskantar matsananciyar yunwa da ke buƙatar kulawar gaggawa.

    Ta ce hakan ya faru ne sakamakon yaƙe-yaƙe da taɓarɓarewar tattalin arziki da gurɓacewar yanayi.

    Shugaban WFP na yammaci da tsakiyar Afirka, Margot van der Velden ya ce miliyoyin rayuka a yankin na cikin mawuyacin hali.

    Raguwar kuɗin da ake bai wa shirin ya sa shi rage ayyukansa tare da rage dubban ma'aikata.

  11. Nijar ta ƙulla alaƙar tsaro da Iran

    Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninta da Iran wajen yaƙi da ta'addanci.

    Haka kuma yarjejeniyar za ta ƙunshi yaƙi da miyagun laifuka da kuma kula da shige da fice ba bisa ƙa'ida ba.

    A jiya ne ƙasashen biyu suka cimma wannan matsaya yayin wata ganawa tsakanin ministan harkokin cikin gida na Nijar da tawagar Iran a ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janarar Ahmad Reza Radan a birnin Yamai.

  12. An kama mutum biyar bisa zargin kashe ƙaramar yarinya bayan garkuwa da ita

    A Najeriya, Gwamnatin jihar Kano ta ce jam’ian tsaron farin kaya na DSS sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da kisan wata ƙaramar yarinya mai suna Sakina Mamuda, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gwarzo.

    Mai Magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin tofa ya ce mutanen sun yi garkuwa da yarinyar ne kuma suka buƙaci biyan kuɗin fansa.

    Sai dai ya ce bayan an biya su kuɗin fansar ne kuma sai kuma suka kashe ta.

  13. Rasha ta yi bikin cika shekara 80 na samu nasara a kan dakarun Nazi na Jamus

    Ƙasar Rasha ta gudanar da wani atisayen soji a birnin Moscow domin murnar cika shekara 80 da fatattakar dakarun Nazi a yaƙin duniya na biyu.

    Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaba Putin ya alaƙanta yaƙin da ƙoƙarinsa na kare ƙasarsa a yaƙinsa da Ukraine, inda ya ce dukkan ƴan ƙasar na goyon bayan yaƙin da ake fafatawa.

    Duk da yunƙurin ƙasashen yammacin duniya na ware ƙasar Rasha saboda yaƙin, sama da shugabannin ƙasashe guda 20 ne suka samu halartar bikin.

    Sai dai a nasa ɓangaren, Shugaban Ukraine Zelensky ya bayyana taron atisayen da "atisayen son-rai"

  14. ACF ta buƙaci ƴan Najeriya su shirya fuskantar ambaliya a bana

    Ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya wato ACF ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ƴan ƙasar da su fara shirin fuskantar ambaliyar daminar bana.

    Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a matsayin martani kan hasashen ambaliya ta shekarar 2025 da hukumar kula da yanayi ta fitar, inda a ciki hukumar ta lissafa garuruwa aƙalla 1,249 a ƙananan hukumomi 176 da ke jihohi 30, ciki har da jihohi 16 na arewa za su fuskanta.

    A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na hukumar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yiwuwar faɗaɗar ambaliyar, da fargabar yadda za ta jawo tsaiko a harkokin rayuwa da walwalar al'umma yankin.

    Ƙungiyar ta ce ta ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na wayar da kan al'umma kan batun ambaliyar, amma ta ce ƙoƙarin bai fito fili sosai ba, musamman a yanzu da damina ta fara kankama.

  15. An kashe mutum biyar a harin bam a Kashmir

    Mutum biyar, ciki har da jariri, sun rasa rayukansu a daren jiya sakamakon harbe-harbe da harin bama-bamai a yankin Kashmir da ke Pakistan ke gudanarwa, kamar yadda ƴansandan Pakistan suka shaida wa BBC Urdu.

    A cewar ƴan sandan, harin ya ci gaba da wakana a sassa da dama na yankin har zuwa ƙarfe 4:00 na safe a ranar Juma’a.

    A ranar Alhamis, Pakistan ta ruwaito cewa mutum 31 ne suka mutu sakamakon harin jiragen yaƙi da harbe-harbe daga Indiya tun daga safiyar Laraba.

    Waɗannan sabbin asarar rayuka sun ƙara yawan adadin waɗanda suka mutu a Kashmir zuwa 36.

  16. 'Za a tsara hanyoyin shigar da kayan agaji Gaza'

    Ambasadan Amurka a Isra'ila, Mike Huckabee ya tabbatar da cewa shirye-shirye sun yi nisa domin samar da sababbin hanyoyin shigar da kayan agaji zuwa Gaza ta hanyar amfani da wasu kamfanoni.

    Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da dokar Isra'ila ta hana shigar da kayan agaji zirin ke cigaba.

    Mr Huckabee ya ce ba za a sanya Isra'ila a cikin ayyukan agajjin ba, amma za ta taimaka wajen samar da tsaro.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata sabuwar gidauniyar aikin agaji a Gaza mai suna Gaza Humanitarian Fund ta wallafa bayani game da shigar da kayan agaji Gaza.

    Sai dai kwamitocin agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce ba za su saka hannu ba.

    Asusun ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yunƙurin zai ƙara jefa yara ƙunci ne, maimakon ya rage musu wahala.

  17. Fafaroma Leo ya jagoranci hudubarsa ta farko

    Fafaroma Leo XIV ya jagoranci ibadarsa ta farko, inda ya gabatar da huduba ta farko a cocin Sistine Chapel, wanda shi ne jagorancin ibadarsa ta farko a matsayin shugaban Cocin Katolika.

    Aƙalla manya-manyan malaman cocin guda 130 daga ƙasashen duniya ne suka halarci zaman, domin sauraron jawabin sabon fafaroman.

    Daga shigowarsa ya sumbaci hasumiyar da ke tsaye a cikin Cocin, sannan ya kewaya yana tattaki.

    Daga nan ne sai ya jagoranci addu'a, inda da farko ya tabbatar da cewa shi ɗan'adam ne mai zunubi, sannan ya nemi yafiyar Allah.

  18. Indiya ta buƙaci a kulle shafuka 8000 a kafar X

    Shafin sada zumunta na X ya bayyana cewa ya kulle shafin mutum 8,000 a Indiya bisa umarnin da ya samu daga gwamnatin ƙasar, a daidai lokacin da rikicin siyasa ke ƙara tsananta tsakanin Indiya da Pakistan.

    Waɗannan shafukan sun haɗa da na kafafen watsa labarai na Pakistan kamar Dawn da Geo TV, da kuma na wasu ƴan jarida daga Pakistan.

    A wani mataki na ɗan lokaci, X ta kuma dakatar da shafin sashen hulɗa da harkokin gwamnatinta a Indiya kafin ta dawo da shi.

    X ya ce wannan mataki na kulle shafukan ba abu ne mai sauƙi, amma an yi hakan ne domin tabbatar da cewa kafar za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga ƴan Indiya.

    X, mallakin Elon Musk, ta bayyana cewa tana bincikar duk wata hanya ta shari’a da za ta iya bi don ƙalubalantar wannan umarni.

  19. Kotu ta yanke wa mai kamfanin cyrpton da ya durƙushe zaman gidan yari a Amurka

    Wata kotu a Amurka ta yanke wa Alex Mashinsky, mamallakin kamfanin cyrptocurrency nan da ya druƙushe, Celsius zaman kurkuku na shekara 12.

    Tun a watan Disamban da ya gabata ne ɗan kasuwar, wanda ɗan asalin Isra'ila ne mazauna Amurka ya musanta dukkan zarge-zarge guda biyu da ake masa.

    Mai shigar da ƙara ya ce Mashinsky ya damfara masu zuba jari, inda ya zambace su da cewa akwai riba sosai a kamfaninsa.

    Da kamfaninsa ɗin ya durƙushe a shekarar 2022, an ruwaito cewa sama da mutum dubu 100 ne kuɗaɗensu ya narke, inda suka yi asarar sama da kadarorin dala biliyan huɗu.