India da Pakistan sun kai wa juna hare-hare

Lokacin karatu: Minti 3

Indiya ta ce ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama a kan wurare cikin Pakistan, a matsayin ramuwar gayya ta harin da wasu 'yan bindiga suka kai yankin Kasmir da ke karkashin ikonta a watan da ya gabata – wanda a lokacin aka kashe fararen hula 26.

Kafafen yada labarai na Pakistan sun bayar da rahoton jerin fashe-fashe a wurare daban-daban ciki har da birnin Muzaffarabad, da har wutar lantarki ta dauke.

Tun da farko Pakistan ta ce mutum takwas sun mutu, yanzu kuma ta ce sun kai 26 tare da raunata 46 a hare-haren.

Wannan rikici ya fara tsananta ne bayan da dangantaka tsakanin kasashen makwabtan juna, masu makaman nukiliya, bayan harin da aka kai wa wasu‚ yan yawon bude idanu a yankin Kashmir bangaren da ke karkashin ikon Indiya mako biyu da ya gabata.

A wadannan hare-hare na yanzu gwamnatin Indiya ta ce ta hari abin da ta bayyana a matsayin wurare da kayayyakin 'yan ta'adda, inda ta ce daga nan ne aka tsara da kuma kai mata wancan hari na baya;

Bahawalpur, birnin lardi mafi yawan al'umma a Pakistan wato Punjab, shi ma yana daga cikin wuraren da Indiya ta kai harin kamar yadda rahotanni suka ce.

Rundunar sojin Pakistan ta fitar da wasu hotuna da ta ce na nuna yadda Indiyar ta kai harin a wannan birni.

Haka kuma India ta kafe cewa ba wasu wurare na sojin Pakistan da ta kai wannan hari.

Wata majiya ta sojin Pakistan ta ce wuraren da aka kai harin sun hada da masallatai, kuma harin ya shafi mutane.

Wakiliyar BBC ta ce rundunar sojin Pakistan ta shaida wa BBC cewa tuni ta fara kaddamar da hare-haren ramuwar gayya har ma ta kakkabo jiragen yakin Indiya biyar da wani marar matuki guda.

Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa an samu asarar Rayuka a Indiya, bayan Islamabad din ta harba makamaman Atilare tsallaken iyakarta da makwabciyar ta ta.

Gwamnatin Pakistan ta fitar da wata sanarwa yanzun nan, tana cewa sojojin Indiya sun daga farar tuta a kan iyaka, alamar sun yi saranda.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin bangarorin biyu kan harin.

Mai magana da da yawun majalisar dinkin duniya y ace babban sakataren majalisar, António Guterres, yad amu matuka gaya kan wannan rikici na soji tsakanin India da Pakistan, kuma ya yi kira ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa.

Shi kuwa Shugaba Donald Trump na Amurka cewa ya yi yana fatan za a gaggauta kawo karshen rikicin tsakanin kasashen biyu masu makamin nukiliya, makwabtan juna.

Ya ce, '' abin kunya ne yanzu muka ji labarin a daidai lokacin da muke shigowa wannan ofis. Mun ji labarin yanzu,. Ina ganin mutane sun san wani abu zai faru, bisa la'akari da dan abin da ke tsakaninsu a baya.

Sun dade suna yaki da juna. Tsawon gomman shekaru da karni suna yaki, idan ka duba. A'a, ina fatan zai kare cikin sauri.''

Zaman tankiya tsakanin kasashen biyu ya tsananta ne tun bayan harin watan da ya gabata, inda India ke zargin Pakistan da mara baya da 'yan ta'adda da ke kai hari yankinta – zargin da Pakistan ta musanta.

Tsawon gomman shekaru yankin Kashmir da ke karkashin ikon India yana fama da rikicin masu tayar da kayar baya – da ya lakume dubban rayuka.

Kowacce daga cikin kasashen biyu na ikirarin cewa yankin na Kashmir nata ne gaba daya.