Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke faruwa a Kashmir kuma me ya sa aka damu da yankin?
Jam'iyya mai mulki ta BJP a kasar Indiya tana kara azama wajen janye wa jihar Jammu da kuma yankin Kashmir alfarmar da suke da ita ta cin gashin kansu, inda suka ce gyara ne ga "kuskuren tarihi".
Wakiliyar BBC Geeta Pandey a Delhi ta yi bayani kan abin da ke faruwa da kuma muhimmancinsa.
Me yasa Kashmir ke jawo ce-ce-ku-ce?
Kashmir yana yankin Himalaya ne, wanda kasashen Indiya da Pakistan suke cewa mallakinsu ne.
A shekarun baya yankin babba ne, wanda ake kira Jammu da Kashmir. Amma ya hade da Indiya a shekarar 1947 lokacin da aka raba nahiyar a karshen mulkin mallakar Birtaniya.
Daga baya ne kuma Indiya da Pakistan suka shiga yaki kan yankin, inda kowacce kasa ta samu iko da wani bangare na yankin bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
An yi ta samun rikici a bangaren da Indiya ke da iko na tsawon shekara 30 saboda fafutikar neman 'yancin kai daga wurin gwamnatin Indiya.
Me ya faru?
A 'yan kwanakin da suka gabata na watan Agustan nan, an ga alamun tashin hankali a Kashmir.
Dubban dakarun Indiya ne aka jibge a yankin sannan kuma aka soke aikin ibadar Hindu mai matukar muhammanci, aka kuma rufe makarantu, aka umarci masu yawon bude-ido da su fice, aka katse layin waya, aka kuma tsare wasu 'yan siyasa.
Sai dai abin da aka fi tsokaci a kai shi ne, za a jingine sashe na 35A da ya bai wa mutanen yankin wasu alfarmomi na musamman.
Kwatsam sai gwamnati ta bai wa jama'a mamaki, inda ta ce za ta daina aiki da ayar doka ta 370 wadda ta kunshi sashe na 35A. Wannan ayar doka ita ce kashin bayan alakar Indiya da yankin na Kashmir a tsawon shekara 70.
Mene ne tasirin ayar dokar 370?
Ayar dokar ta bai wa jihar damar cin gashin kanta wadanda suka hada da yin kundin tsarin mulkinta da tutarta da dokokinta. Sai dai harkokin kasashen waje da na tsaro da na sadarwa za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon gwamnatin tarayya.
A saboda haka ne, Jammu da Kashmir suke iya samar da dokokin da suka shafi takardar zama ta dindindin da mallakar gida da kuma hakkoki.
Sannan kuma za ta iya haramta wa 'yan kasar Indiya mallakar gida ko kuma ma zama a yankin.
Tanadin kundin tsarin mulkin Indiya ya tallafi alakar Indiya da Kashmir mai cike da rikici, wanda shi ne yaki guda daya da Musulmai ke da rinjaye da ya yarda ya kasance a Indiya.
Me yasa gwamnati ta dauki matakin?
Firaministan Indiya Narendra Modi da kuma jam'iyyar Janata Party ta 'yan kishin kasa sun dade suna adawa da ayar dokar Article 370, kuma soke sashen daga kundin tsarin mulki yana cikin manufofinsu a zaben da ya gabata.
Sun hakikance cewa ya kamata a soke sashen domin a shigo da Kashmir cikin Indiya kamar sauran sassan kasar.
Bayan ta samu gagarumar nasara ne a zaben, gwamnatin Modi ba ta yi wata-wata ba wajen fara aiwatar da alkawarin da ta dauka.
Masu sukar wannan yunkuri suna alakanta hakan da matsalolin tattalin arziki da Indiyar ke fuskanta.
Akasaarin 'yan Kashmir suna ganin cewa yunkurin na rage wa al'ummar Musulmi yawa ne ta hanyar bai wa sauran Indiyawa damar sayen gidaje a yankin.
Duk da cewa sanarwar da ministan harkokin cikin gida Amit Shah ya bayar a majalisa ta bai wa jama'a mamaki, zai dauki gwamnati tsawon lokaci kafin ta kammala yanke hukunci.
Kazalika, wannan ya yi daidai da manufar Mista Modi da yake so ya nuna wa 'yan kasa cewa jam'iyyarsa ta BJP ba ta sassauci kan Pakistan da Kashmir.
Wanne sauyi aka samu?
Kashmir za ta rasa kundin tsarin mulkinta, sai dai ta ci gaba da amfani da na Indiya kamar kowacce jiha a kasar.
Duk wata doka ta Indiya za ta shafi 'yan Kashmir sannan kuma wasu da ba 'yan Kashmir din ba za su iya sayan gidaje a yankin.
Gwamnati ta ce hakan zai kawo ci gaba ga yankin.
"Ina son jama'a su san irin barnar da Articles 370 da 35A suka yi mana," Mista Sha ya fada a majalisa.
"Saboda wadannan ayoyin dokar ne har yanzu ba a taba gudanar da cikakkiyar dimokuradiyya ba, cin hanci ya yawaita a garin, sannan kuma babu ci gaban da za a samu."
Sannan kuma gwamnati na son ta raba jihar zuwa jihohi guda biyu karkashin kulawar gwamnatin tarayya, yankin zai hada da Jiha daya mai rinjayen Musulmai dayar kuma mai rinjayen Hindu 'yan Jammu.
Daya bangaren kuma na Ladakh 'yan addinin Buddha ne ke da rinjaye, wanda a tarihi yake kusa da Tibet.
Ko hakan yana kan doka?
Kundin tsarin mulki ya tanadi cewa ba za a iya sauya ayar dokar Article 370 ba har sai da amincewar "gwamnatin jiha."
Sai dai kuma babu wata tabbatacciyar gwamnati a Jammu da Kashmir cikin sama da shekara guda yanzu.
Gwamnatin Indiya ta so maye gurbin kundin tsarin mulkin da na gwamnatin tarayya bayan an kayar da gwamnatin Mehbooba Mufti a zabe.
Saboda haka, gwamnatin tarayya tana bukatar samun goyon bayan gwamnan yankin ne kawai, wanda dama shi ne ya kaddamar da kundin tsarin mulkinta a yankin.
Gwamnatin ta ce tana da damar yin hakan a doka. Sai dai kan masana ya rabu.
Wata kwararriya kan tsarin mulkin kasar Subhash Kashyap ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa "matakin yana kan doka sannan kuma babu wata matsala a ciki".
A gefe guda kuma, wani masanin AG Noorani ya shaida wa sashen Hindi na BBC cewa "ba ya kan doka kuma daidai yake da zamba", wadda za a iya kalubalanta a gaban kotun koli.
'Jam'iyyun adawa ka iya kalubalantar matakin amma maganar Kashmir abu ne mai girma ga Indiyawa.
Sai dai akasarinsu ba za su so su yi adawa da matakin ba domin gudun kar a kalle su a matsayin makiyan Indiya.
Yanzu sai dai a bar sauran 'yan kasa su yanke hukuncin daukar matakin kalubalanatar shirin.