Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra'ila ta ɗau alwashin ci gaba da kai farmakin soji a Gaza har sai ta cimma burinta
Rundunar sojin Isra'ila ta ɗau alwashin ci gaba da gwabza yaƙi a Gaza, sai dai ta amince da cewa yaƙin yana da ''wahala'' kuma ba ya "sauri".
Wani mai magana da yawun sojojin ya bayyana a karshen mako cewa suna faɗaɗa farmaki ta ƙasa a kudanci da kuma arewacin Zirin Gaza''.
A gefe guda kuma, Amurka ta ce Shugaba Biden ya yi magana da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kuma "ya jaddada buƙatar" kare rayukan fararen hula.
A martanin da ya mayar, Netanyahu ya ce za su ci gaba da yaƙin har sai sun cimma dukkan muradan da suka sa a gaba.
Shugaba Biden ya kuma faɗa wa manema labarai cewa bai yi magana da mista Netanyahu kan buƙatar tsagaita wuta ba.
A ranar Juma'a, Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da kudirin buƙatar shigar da kayan agaji zuwa Gaza - amma bai yi magana kan batun tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu da ke faɗa da juna ba.
Zaman tattaunawa da aka yi a Masar a farkon makon nan da nufin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, ta ƙasa haifar da ɗa mai ido zuwa yanzu.
Wani jami'in Falasɗinawa a zaman tattaunawar, ya faɗa wa BBC cewa Masar ta gabatar da matakai guda uku wanda zai fara da sahirta faɗa na makonni biyu don kai kayan agaji da faɗaɗa ta zuwa mako uku ko huɗu a gaba, da kuma sakin 40 daga cikin mutanen da ake tsare da su, da suka haɗa da mata da ƙananan yara.
A nata ɓangaren Isra’ila za ta saki fursunoni 100 daga cikin waɗanda take tsare da su.
Wannan matakin zai biyo baya da kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai duba batun jin kai da kuma sake gyara wuraren jama'a, da tsagaita wuta na dindindin da kuma musayar fursunoni.
Ma'aikatar lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas, ta ce an kashe mutum sama da 20,000 da kuma jikkata 54,000 a Gaza tun soma yaƙin. Yawancin waɗanda aka kashe sun kasance mata da yara, a cewar Hamas.
Isra'ila ta ce ta ɗauki matakai don ganin faɗan bai ritsa da fararen hula ba, inda ta ɗora laifi kan Hamas saboda ɓoye wa cikin yankunan da ke da ɗimbin jama'a.
A gefe guda, ma'aikata tsaron Isra'ila ta sanar da cewa an kashe sojojinta 14 a ranar Juma'a waɗanda ke yaƙi a Gaza, wanda ya kawo jimillar dakarunta da aka kashe a cikin Gaza zuwa 150.
Da yake mayar da martani kan mutuwar sojojin, Mista Netanyahu ya bayyana a ranar Lahadi cewa Isra'ila na shan wuya a yaƙin, amma babu wani zaɓi illa ci gaba da faɗa.
Isra'ila ta ce ta kama mayaƙan Hamas 700 tun bayan da ta fara kai hare-hare da zimmar kawar da ƙungiyar.
Isra'ila ta fara kai hare-hare ne bayan da mayakan Hamas suka tsallaka daga Gaza zuwa kudancin ƙasar a ranar 7 ga Oktoba, tare da kai hari mafi muni inda suka kashe mutum 1,200 da kuma garkuwa da 240.
Mista Netanyahu da mista Biden sun tattauna ta wayar tarho kan farmakin Isra'ila a Gaza ranar Asabar.
A bayanai da ta fitar a ranar Lahadi, ma'aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon Hamas, ta ce an kashe akalla mutum 166 da jikkata 384 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin lugudan wuta a Gaza - inda suka umarci fararen su tsere.
A ranar Asabar, rundunar sojin ta ce ɗaya daga cikin jiragenta na yaƙi ya kashe wani mutum da take zargin yana safarar makamai zuwa Gaza don bai wa Hamas mai suna Hassah Atrash. Babu wani tabbaci kan hakan daga Hamas.
Sojojin sun ce suna da ikon kusan ɗaukacin arewacin Zirin Gaza, kuma tana faɗaɗa samamenta a kudanci.
Wani mai magana da yawun sojojin ya ce suna samun kutsawa cikin yankunan da Hamas ke da karfi a kudancin Gaza.
Da yake yi wa muƙarrabansa ƙarin haske a ranar Lahadi, Mista Netanyahu ya musanta batun cewa
MDD ta ce mutum 150,000 ne aka kwashe a tsakiyar yankin Gaza.
Da yake jawabi ga majalisar ministocinsa a ranar Lahadi, Mista Netanyahu ya musanta cewa shugaban Amurka ya ba shi shawarwari game da ƙara faɗaɗa ayyukan soji.
Jaridar Wall Street Journal ta rawaito cewa an yi magana da Mista Netanyahu kan harin da aka kai wa kawancen Hamas a Lebanon, wato ƙungiyar Hezbollah.
Wani mai magana da yawun gwamnati ya shaida wa BBC cewa "halin da ake ciki a arewa... abu ne da ba za a iya jurewa ba" kuma Isra'ila tana "ƙoƙarin hana Hezbollah janyo mu cikin yaƙi".
Ya ƙara da cewa "Za mu ci gaba da yin shirye-shiryen da suka dace domin dakile wannan barazana daga kan iyakar arewa."