Wane ne Robert Prevost, Fafaroma Leo na 14?

Lokacin karatu: Minti 4

Dandazon mutane sun ɓarke da sowa a lokacin da farin hayaƙi ya bayyana a wani bututu da ke saman Babban Cocin Kotolikan da ke alamta zaɓar sabon fafaroman.

Manyan limamanin Cocin masu muƙamin Cardinal ne ke zaɓar fafaroma, sannan sai an samu kashi biyu bisa uku na manyan limaman kafin a ayyana wanda ya yi nasara.

A jawabinsa na farko bayan zaɓarsa, Fafaroma Leo 14 ya yi kira da mabiya ɗariƙar Katolika su yi aiki tare ta hanyar amfani da tattaunawa don haɗa kan al'ummar duniya ta hanyar samar da zaman lafiya.

An haifi Fafaroma Leo na 14 a birnin Chicago na Amurka, kodayake asalin iyayensa ƴan Italiya ne, asalin Faransa da Sifaniya.

Ya na da shekara 69, kuma shi na fafaroma na 267 da ya meye gurbin wannan kujera.

Shi ne BaAmurke na farko da ke hawa wannan kujera ta Fafaroma.

Robert Prevost ya halarci babbar makarantar sakandire da Cocin St Augustine ke gudanar da ita.

A haife shi a a shekarar 1955 a Chicago,a yayin da kuma ya kai shekara 27 ya tafi birnin Roma domin faɗaɗa karatunsa.

Ya shafe shekaru masu yawa yana ayyukan da suka shafi addini a ƙasar Peru kafin daga baya aka ba shi muƙamin archbishop na Chiclayo.

A shekarar 1982 ne ya soma ayyukan addini, kafin daga bisa ya koma Peru inda yayi shekara uku sannan ya zama Fasto a Amurka.

Fafaroma Leo XIV na magana da yaruka da dama ciki har da turancin Ingilishi da Italiyanci.

Waɗanda suka san shi, sun ce yana da ɗabi'ar sauraron jama'a.

Ya shafe shekaru 10 yana aikin limamin coci da kuma koyarwa a wani yanki da ke Trujillo a arewa maso yammacin Peru.

Shekara biyu da suka gabata ne marigayi Fafaroma Fransis ya naɗa shi a muƙamin mai ba shi shawara wajen naɗa sabbin masu muƙaman bishop a faɗin duniya.

Ya taimaka wajen gina coci-coci da inganta hanyoyin isa cocinan da ke yankunan karkara.

Mene ne ra'ayoyin Fafaroma Leo Robert Prevost

Ana ganin Fafaroma Prevost na da irin ra'ayoyin da Fafaroma Francis ke da su game da 'yan gudun hijira da talakawa da kuma muhalli.

Wani tsohon ɗan dakinsa, Reverend John Lydon, ya bayyana wa BBC cewa "Prevost mutum ne mai son jama'a, mai sauƙin kai, kuma "mai damuwa sosai da talakawa."

A kan asalin rayuwarsa, Prevost ya shaida wa gidan talabijin na Italiya, Rai, kafin zabensa, cewa ya tashi ne cikin iyalin 'yancirani.

"An haife ni a Amurka, amma kakannina duka 'yancirani ne — Faransawa da Sifaniyawa. Na tashi a cikin iyali mai tsananin bin addini kuma iyayena biyu suna da matuƙar shiga harkokin cocin unguwarmu," in ji sabon Fafaroma.

Duk da cewa an haife Prevost a Amurka, Vatican ta bayyana shi a matsayin Fafaroma na biyu daga nahiyar Amurka (na farko shine Francis daga Argentina).

Ya kasance wanda yake yawan faɗin alkhairin marigayi Francis da ya gada.

Sannan sabon Fafaroma mutum ne da ake yawaita faɗan kyawawan halinsa da dabi'u. Duk da cewa kashi 80 cikin 100 na masu zaɓan Fafaroma, Francis ne ya basu muƙaman saboda haka ba abin mamaki ba ne ganin su zaɓi Prevost.

Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra'ayi, wadda zai cigaba da tafiyar da ayyuka da sauye-sauyen Fafaroma Francis a cocin Katholika.

Duk da cewa shi ɗan Amurka ne, yana sanne da rabuwar kawunan da ake da shi a cocinsu, sannan asalinsa na latin Amurka ana ganin zai taimaka wajen tafiyar da harkokin cocin ganin wanda ya rasu daga Argentina ya fito.

Amma fa lokacin da yake shugabanta coci a Peru bai tsallake zarge-zargen cin zarafi ta hanyar lalata da ya mamaye cocin ba, koda yake mukarabansa sun sha musanta zargin.