Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Martanin APC kan 'yanadawan da suka kafa gwamnatin je-ka-na-yi-ka
Jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta mayar da martani game da wata gwamnatin je-ka-na-yi-ka da wasu 'yan adawar siyasa suka kafa, da nufin kalubalanta da yin gyara ga manufofin gwamnatin kasar.
Matakin da jam'iyyar ta ce bai girgiza ta ko daga mata hankali ba, domin kuwa mataki ne na bigi-bagiro kawai, wato tamkar wani hotoho ne kawai.
Sai dai masana na ganin wannan gwamnatin ta je-ka-na-yi-ka, wadda akan yi irin ta a wasu kasashe, za ta wata sabuwar hanyar zaburar da gwamnatin kasa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al'umma.
Martanin na jam'iyar APC mai mulkin Najeriya, yana zuwa bayan da wani fitaccen masanin tattalin arziki, kuma dan gwagwarmayar siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi ya bude wani sabon shafin salon hamayyar siyasa a kasar, ta hanyar kafa gwamnatin je-ka-na-yi-ka.
Inda ya nada 'ya'yan wasu jam'iyyun hamayya kan mukaman gwamnati irin na dodorido.
Bala Ibrahim, daraktan watsa labarai na kasa na jam'iyyar ta APC, ya ce adawa ce da ba zata yi tasiri ba, iya dai kawai su yi haushi, amma babu wani abu na tada hankali.
"Ai ba su da wannan hurimi, saboda baa gwamnati sai bangarori uku sun hadu.
"Sannna babu wani abin tsoro saboda dama haka ake son dimokuradiyya a samu wadanda za su rika kalubalantar salon mulki domin samun wanzuwa da cigaba a gwagwarmayar biya bukatun al'umma", in ji Bala Ibrahim.
Me masana suka ce?
Sai dai masana irin su Farfesa Abubakar Umar Kari na jami'ar Abuja, suna ganin wannan wata sabuwar dabara ce ta 'yan adawa.
Farfesa Kari ya ce, wannan salo ba wani sabo abu ba ne domin akwai kasashen duniya da ke irin haka.
"Kuma indai saboda adawa aka kirkira ta babu wata matsala tunda bisa doka da tsari na mulki bai haramta ba.
"Indai da zuciya daya cikin mutunci da daraja za su yi abu ne mai kyau da zai karfafa demokuradiya a Najeriya. Sannan wani yanayi ne da zai sa APC ta kasance cikin shiri a kodayaushe."
Ana dai kallon wannan kafa gwamnatin je-k-na-yi-ka da Farfesa Pat Utomi ya yi, a matsayin wani karin tsokci game da hankoron da 'yan bangaren hammayar siyasar Najeriya ke ta yi, da nufin yi wa jam'iyyar APC da gwamnatinta kofar rago, don karbe mulki a zaben shekara ta 2027.