Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko gwamnatin jiha a Najeriya na da ikon yi wa gidajen rediyo iyaka?
Sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Najeriya, na 1999 ya yi tanadin cewa, dole ne kodayaushe kafafen yaɗa labarai da suka hada da gidajen rediyo da talabijin da sauransu, su kasance masu 'yancin kiyaye muhimman manufofin ƴancin faɗin albarkacin baki.
Sashen ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai ƴancin gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.
Haka kuma sashen ya kare ƴancin faɗin albarkacin baki, tare da tabbatar da cewa kowane mutum na da damar bayayana ra’ayinsa ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Dakta Sulaiman Santuraki, malami a makarantar horas da lauyoyi ta Najeriya da ke Yola, ya ce akwai wasu wurare da gwamnatin jiha ke da hurumin taka wa gidajen rediyo birki.
''Duk da ƴancin da kundin tsarin mulki ya bai wa kafafen yaɗa labarai, ƴancin faɗar albarkacin baki, amma akwai wasu iyakoki da kundin tsarin mulki ya bayar da damar hakan'', in ji shi.
Lauyan ya ce sashe na 45 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya bayar da damar cewa idan aka yi wata doka a tsarin mulkin dimokradiyya domin kiyaye tsaro da lafiyar jama'a, to gwamnatin jiha na da hurumin taka wa gidajen rediyo birki.
''Don haka idan gwamnatin jiha ta fahimci gidajen rediyon na yin wani abu da ka iya zama barazana ga zaman lafya da tsaron al'umma, to babu laifi ta hana su yin wannan abu'', kamar yadda malamin makarantar lauyoyin ya bayyana.
A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da haramta yaɗa shirye-shiryen siyasa kai-tsaye a gidajen radiyon faɗin jihar a wani mataki na tsaftace ''aikin jarida''.
Gidajen radiyo musamman a jihar Kano sun yi fice wajen tsara shirye-shiryen siyasa kai-tsaye, da nufin bai wa al'umma damar faɗin albarkacin bakunansu.
Wannan batu na daga cikin abubuwan da suka haifar da samuwar ''Sojojin Baka'' a Kano, wato ƴan siyasa da ke shiga gidajen rediyo domin kare muradun iyayen gidansu.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labaran jihar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne domin, hana yaɗuwar kalamai na cin mutunci da ɓata suna.
Matakin ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan ciki da wajen jihar, lamarin da ya sa ƴan hamayya ke zargin gwamnatin da yunƙurin toshe bakunansu ta tauye ƴancin faɗin albarkacin baki.
Siyasar Kano na ɗaya daga cikin masu zafi a faɗin Najeriya saboda yadda jihar ke da yawan al'umma da kuma ƴansiyasa.
To sai dai ana zargin ƴan siyasar jihar da cin mutuncin juna ta hanyar amfani da gidajen radiyo da ke faɗin jihar.
Inda ake zargin wasu manyan ƴansiyasar jihar da ɗaukar nauyin sojojin bakan, domin su ci mutuncin abokan hamayyarsu.
Haka ma akwai masu zargin cewa akwai wasu gidajen rediyon sun dogara da shirye-shiryen siyasa wajen samun kuɗi.
Me dokokin NBC suka ce game da shirye-shiryen siyasa?
Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai na Najeriya ta tanadi dokoki da ƙa'idojin da ya kamata gidajen yaɗa labarai su bi wajen gabatar da shirye-shiryen siyasa.
Daga ciki akwai dokar da ta tanadi cewa dole ne gidan radiyo ya tabbatar da adalci da ji daga kowane ɓangare a lokacin gabatar da wata hira da ta shafi wani zargi a siyasance, ta hanyar jin ta bakin ɗaye gefen.
Sannan dole waɗanda za su shiga tattaunawar su kasance masu matsayi ko mataki iri guda
''A lokacin gabatar da shirye-shiryen da suka shafi siyasa, dole ne a ƙaurace wa kalaman ƙiyayya da kalaman zagi ko cin mutunci ko kalaman da za su harzuƙa jama'a ko na ɓata-suna''.
''Dole ne a bai wa kowace jam'iyya ko ra'ayi lokaci daidai da wanda ta bai wa ɗayar domin tabbatar da daidato, musamman lokutan yaƙin neman zaɓe''.
Me gidajen rediyo a Kano ke yi da ya saɓa doka?
Takardar sanarwar bayan taron da aka gudanar tsakanin Hukumar kula da gidajen radiyo ta Najeriya, NBC da wakilan kafafen yada labarai a jihar Kano cikin watan Afrilun da ya gabata, wadda BBC ta gani ta nuna cewa akwai kura-kurai masu yawa da wasu gidajen rediyon jihar ke tafkawa da kuma suka sa ba wa doka.
Kurakuran sun hada da:
Karuwar yaɗa kalaman cin mutunci da ɓata suna a shirye-shiryen siyasa da gidajen rediyon jihar ke yi.
''Ƙaruwar shirye-shiryen siyasa a Kano za su iya zama barazana ba ga ba ma fannin siyasa kawai ba, har ga tsaro da haɗin kan al'ummar Najeriya idan ba a magance ta ba'', kamar yadda sanarwar bayan taron da NBC ta fitar.
Haka kuma sun gano cewa ƙaruwar ''Sojojin baka'' na ci gaba da rage wa Kano ƙima cikin sa'anninta jihohi, kuma mutanen Kano sun zuba idanu ba sa cewa komai kan batun.
Wasu gidajen rediyon ba sa bai wa kowane ɓangare damar kare kai daga zarge-zarge ƴansiyasa, wanda kuma hakan ya saɓa wa dokokin NBC, da kuma tabbatar da ƴancin faɗin albarkacin baki.
Sun kuma gano cewa gidajen rediyo na ɗaya da cikin mafiya tasiri a zukatan al'ummar jihar, inda mutane ke saurin yarda da maganganun da aka faɗa a gidan rediyo.
Takardar ta nuna cewa a dalilim haka hukumar NBC da kafafen yada labaran sun amince da shawarar dakatar da yaɗa shirye-shiryen siyasa kai a gidajen rediyon faɗin jihar.
Haka kuma NBC ta amince cewa dole ne kafafen yaɗa labaran jihar Kano su riƙa amfani da dokokin hukumar NBC a matsayin madogara wajen gudagar da ayyukansu bisa tsarin dokokin da hukumar ta tanadar.