Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi nasarar raba kan ƴan Arewa - Shekarau
A Najeriya, ana ci gaba da samun yunƙuri daga ƙungiyoyi da rukunin masu faɗa-a-ji da ke gangami da shirya taruka kan mawuyacin halin da yankin arewacin kasar ke ciki, a shekarun baya-bayan nan.
A yan kwanakin nan ne dai aka sami wata ƙungiya ta masu rajin farfaɗo da ruhin dimokraɗiyya a arewacin Najeriyar mai suna Northern Democrats League a ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Kano Dr Mallam Ibrahim Shekarau.
Ƙungiyar wadda ta fara kai ziyara ga fitattun manyan ƴan Nijeriya, ta ce ta damu matuƙa da taɓarɓarewar al'amura a kusan dukkanin fannonin rayuwa a arewa.
Kamar dai yadda shugaban ƙungiyar Mallam Ibrahim Shekarau ya shaida wa BBC, ya ce sun yanke hukucin kafa ƙungiyar ne saboda halin da Dimokaradiyya ke ciki a yankin arewacin Najeriyar na koma baya.
Mallam Shekarau ya ce “Mun fi shekaru biyu muna tattauna kan yadda kasa ta lalace, yadda ake zaben shugabanin ya lalace, yadda aka mayar da zaɓe dauki dora, da koma baya da ake fama da shi a fanin hadin kai yasa muka yanke hukuncin daukar mataki na kawo gyara a wannan ɓanagare” in ji shi.
‘Daya daga cikinmu ya nemi dai-daikunmu da bamu fi 50 ba, bayan mun zauna aka dora shugabancin a kaina, yanzu mun kai kusa mu dari hudu da hamsin, inda aka mata lakabi da ƙungiyar Masu kishin gyaran dimokaradiya a arewacin Najeriya” a cewar Mallam Ibrahim Shekaru.
Har ila yau tsohon gwamnan na Kano Ibrahim Shekarau ya ce burinsu shi ne “samar da hadin kan al’ummarsu, da maganar bayar da ingantacen ilimi musamman ganin irin gorin bara da almajirci da ake yi mana, wanda da mun tsaya mun dauki matakin da ya kamata da tuni mun yi nisan da ya kamata, a bangaren ilim, da kuma sauran matsaloli da yankin namu ke fama da shi”
Ya ce suma jam’iyyun na da hannu a cikin halin ni ƴasu da ake fama da shi a kasar, saboda yadda suke marawa wadan da basu fahimci yadda ake shugabanci ba.
“Shi yasa muka fara sanar da iyayen kasa irin su Obasanjo, su Babangida har da shi shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da irinsu T. Y Danjuma da mai alfarma Sarkin Musulmi, kan abun da muke yi, da kuma sanar da su matakan da muke ganin an bi don magance matsalar da yankin arewacin Najeirya ya ke ciki, tare da dakile bambamcen addini, da kabilanci da shi kansa halin tsaron nan da muke fama” in ji Mallam Ibrahim shekarau.
Haka kuma ya ce suna shirya wani taro da za a gudanar da shi a Kaduna, wanda tuni suka kafa kwamitoci, kuma za su gayyato masana don zasu yi fashin baƙi kan irin waɗan nan matsaloli, da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi.
Si dai mallam shekarun ya ce ba wai sun raina ƙoƙarin da ƙungiyar nan ta Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya ta ACF da ta Dattawan Arewacin yankin Northern Elders Forum bane, za su yi aiki tare da su musamman ma ganin yadda suke da bayanai da littattafai da aka tara kan wadannan matsaloli.
A ranar Talata ne wata tawagar mutum 20 ta shugabannin arewacin Najeriya ƙarkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau suka gana da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta.
Tawagar dai ta je gidan tsohon shugaban na Najeriya da manufar lalubo hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye arewacin Najeriya da ma faɗin ƙasar baki ɗaya.