Yadda 'sojojin baka ke wuce gona da iri a gidajen rediyon Kano'

Lokacin karatu: Minti 3

A jihar Kano, gidajen radiyo na neman zama wani fagen yaƙin cacar baka ga ƴan siyasa, inda lamarin ya kai matsayin da wasu na barin batutuwan gundarin siyasa suna komawa taɓa mutuntaka ko cin mutunci.

Waɗannan ƴan siyasa dai ana kiransu da suna 'Sojojin Baka' suna shiga gidan radiyo ta cikin wasu shirye-shiryen siyasa suna suka ko yabon gwaninsu a siyasance kuma wasu lokutan ba tare da la'akari da abin da ka-je-ya-zo ba.

Sojojin baka sune waɗanda ke kan gaba wajen kare muradan manyan ƴan siyasa a gidajen radiyo da kuma kofofin sada zumunta na intanet.

To sai dai a baya-bayan nan lamarin wasu daga cikin sojojin bakan na ci gaba da ɗaukar wani salo, saboda yadda wasu ke barin batun siyasa suna taɓa mutuncin wani ko wasu a matsayin siyasa.

Malam Kabiru Sufi malami ne kuma masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya shaidawa BBC cewa kalaman cin mutunci tsakanin ƴan siyasa sun yi zafi.

'' Zafin da za a iya cewa abun ya wuce suka da yabo kaɗai, abin ya tafi wani matsayi na taɓa mutuntaka ta su manyan ƴan siyasa. Koda yake wasu suna ganin kamar abu ne na ƙoƙarin nuna cewa mahaukacin gidana ya fi na gidanka kuma yin hakan ƙoƙarin jawo alumma baya ne'' in ji shi

Shi kuwa Farfesa Sule Yau Sule ƙwararre kan harkokin yaɗa labarai da hulda da jama'a da ke jami'ar Bayero da ke Kano, cewa yake a haƙiƙanin gaskiya abubuwan da wasu sojojin baka ke yi ba ya cikin ƙa'idojin magana a kafofin yaɗa labarai.

'' Ko dai ka fito ka yi magana watau abinda ake kira Mass communication watau za ka yi Magana da allumma dayawa, ya fita daga tsarinsa, ya fita daga dokoki ya fita daga ƙa'ida''

''Amma ni a nan babban masu laifi su ne masu gidajen rediyo domin in ba su yarda ba, ba za a yi ba, sannan ba bu dokoki masu ƙarfi wanda za su hukunta shi mai magana da kuma gidajen rediyo'' in ji shi

Farfesa Sule ya ƙara da cewa akwai dokokin hukumar NBC wadda ke sanya ido kan kafafen watsa labaran Najeriya, amma dokokin suna buƙatar a yi musu garambawul.

''Misali idan ka yi maganar za a ce za a ci tararka, kuɗin ƙarshe da za a ci tarar gidan rediyo wanda na sani ba ya wuce naira dubu ɗari biyar''

Da aka tuntubi Aminu Maidawa Fagge wani fitaccen mai magana a shirye-shiryen siyasa a gidajen radiyo a Kano, akan ko me yasa wasu daga cikinsu ke wuce makaɗi da rawa? Sai ya ce:

''Mu ma kanmu abin ba ya yi muna daɗi, domin idan ka kali yaron da zai fito ya ce wani abu a harka ta siyasa. In ka kalli shekarunsa za ka san cewa gaya masa aka yi''

Gidajen rediyon na cikin sahun wadanda ake zargi da kau da kai wajen sukurkucewar wannan lamari. Alhaji Nafiu Yahaya wanda shi ne sakataren ƙungiyar shugabannin kafafen watsa labarai na Kano, ya shaidawa BBC cewa suna iya ƙoƙarinsu wajen ɗaukar mataki akan waɗanda ke wuce gona da iri

'' Muna iya yin mu wajan ganin cewa mun kiyaye dukannin abin da zai fita, abu na biyu shi ne yawancin abun da ke faruwa a wannan lokaci shi ne, za ka ga abu ne da ake yin shi a kafofin sada zumunta inda mutum zai je kai tsaye a sa masa kamara ya riƙa magana kuma ba a tantancewa

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumar NBC wadda ke kula da kafafen watsa labaran Najeriya game da wannan batu, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Masana da dama dai, na tabbatar da cewa tsaftace kalaman ƴan siyasa tamkar tsaftace sha'anin shugabanci ne baki ɗaya, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai shugabanni da jagororin ƴan siyasa sun haɗa kai.