Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Legas

A ranar 18 ga watan Janairu ne al'ummar Najeriya ke gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28, da kuma na majalisar dokokin jiha a faɗin ƙasar.

Legas ce jiha mafi yawan mutanen da suka yi rajista domin kaɗa ƙuri'a, inda take da 7,060,195.

Bugu da ƙari jihar na da ƙananan hukumomi 21.

Za ku iya ganin sakamakon zaɓen gwamnonin sauran jihohin na Najeriya a ƙasa: