Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya: Nazari kan ƙorafin ƴan hamayya game da zaɓen da aka yi wa Bola Tinubu
An bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya bayan wata fafatawa mai zafi, sai dai wasu da dama ciki har da 'yan takarar shugaban ƙasar da suka fafata da shi, kan cewa an yi maguɗi.
Sun yi kira da a soke duka zaɓen, suna zargin cewa Hukumar Zaɓe, INEC, ta karya dokar tattara sakamakon zaɓen saboda ta taimaka wa Tinubu.
INEC ta musanta wannan zargi haka kuma jam'iyyarsa ta APC.
Ta ɓangaren jam'iyyun hamayya har yanzu ba su gabatar da wata ƙwakƙwarar hujja ba kan zarge-zargensu.
Sai dai ɗan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi wanda ya zo matsayi na uku a zaɓen ya ce, zai je kotu domin a ƙwace nasarar da Tinubu ya samu, saboda a cewarsa tasa ce. Amma shi kansa babu wata hujja da ya gabatar.
Abin da ake ta rikici a kansa shi ne na'urar da aka gabatar domin karɓar sakamakon zaɓen wadda ake kira BVAS, wadda aka yi tsammanin za ta sauƙaka maguɗin zaɓen da ake yi a zaɓen Najeriya, ya kuma sanya zaɓen ya zama mai sahihanci.
Ƙorafe-ƙorafen da ake yi na cewa ma'aikatan hukumar sun gaza tura sakamakon zaɓen daga rumfunan zaɓensu zuwa rumbun tattara zaɓe na INEC, wanda hakan ya janyo ƙorafin cewa kamar da haɗin bakin hukumar domin a yi maguɗi.
An fara shiga fargabar cewa za a yi maguɗi ne a safiyar ranar zaɓen, bayan da wani fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta na intanet ya ce ana zargin masu kutse sun ƙwace rumbun da aka tsara za a riƙa tura sakamakon daga rumfunan zaɓe.
Da BBC ta yi bincike sai ta gano cewa shafin da ake magana na INEC ne, ba shi ba ne aka yi wa kutsen, domin ta gano cewa shafi ne aka ƙirƙira kamar na INEC ɗin. INEC da kanta ta ce rumbun nata na nan ƙalau babu kuma wanda ya isa ya yi mata kuste a ciki.
Daga baya da aka ci gaba da samun wannan matsala, sai manyan jam'iyyun siysa irin su PDP da LP suka yi zargin cewa an karya ƙa'idar da aka shimfiɗa ta aike sakamakon zuwa rumbu.
Hukumomin INEC ne suka fito da dokar cewa za su riƙa ɗaukar hoton sakamakon su aike da shi daga rumfunan zaɓe sama da 175,000 da ke faɗin ƙasar, bayan duka jam'iyyun sun sanya hannu kan amincewa da hakan.
Lokacin da suke ƙorafi a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa tsakanin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP da na LP sun yi zargin cewa ko dai an haɗa baki da INEC ta taimaka wa jam'iyya mai mulki ko kuma intanet ɗinsu ta katse.
"Idan tsarin intanet ɗin shafin ne ya samu matsala mun san da wannan, don haka sai a ɗage zaɓen, in kuma ba haka ba, su ne suka ƙi cika alƙawarinsu na aikawa da sakamakon ta intanet.
Wanda hakan na nufin ke nan an haɗa kai da su, sun zama ke nan sun ɗauki ɓangare ke nan ba za su taɓa zama masu adalci ba," in ji Okowa.
INEC ta bayar da haƙuri kan abin da ta kira "matsalar intanet", ta kuma ce duk inda aka samu saɓani tsakanin sakamakon da aka samu na takarda da kuma na intanet za a bincika a gano gaskiya.
INEC ta yi zargin cewa an yi jinkirin da aka samu ya wuce iyaka ne sakamakon matsalar intanet a wasu rumfunan zaɓen.
Da yawa sun yi ƙorafin suna iya aika sakamakon zaɓen 'yan majalisa cikin sauki amma aka samu jinkira wajen aika na shugaban ƙasa, wanda kuma INEC ba ta ce komai ba a kan hakan.
A wani ƙorafi da wakilin babbar jam'iyyar hamma, PDP Dino Melaye ya yi, ya ce an yi aringizon ƙuri'a a jihar Ekiti - jihar da aka fara gabatar da sakamakonta, wadda kuma Tinubu ya samu nasara cikinta, wannan ne ya sanya Dino ficewa daga ɗakin tattara zaɓen.
Sai dai shugaban hukumar zaɓen ya musunta wannan zargi yana cewa adadin masu kaɗa ƙuri'ar da aka tantance bai kai yawan waɗanda suka kaɗa kuri'ar ba, kuma jihar da ma waje ne da Tinubu yake da ƙarfi.
Da yake mayar da martani kan sakamakon zaɓen Ekiti da wasu ke cewa an wallafa shi kwanaki biyar gabanin ranar zaɓen sai shugaban INEC ya ce wannan "labarin ƙanzon-kurege ne."
A ranar Alhamis 02 ga watan Fabarairu, ɗan takarar PDP a zaɓen, Atiku Abubakar ya ce za su ƙalubalanci zaɓen.
Hotunan bidiyo da aka riƙa yaɗawa na yadda ake yi wa masu kaɗa ƙuri'ar barazana tare da ƙwace takardun yin zaɓen da su, an samu rikici a wasu rumfunan zaɓe, musamman a manyan jihohi irinsu Legas - inda Obi ya ci da kuma jihar Rivers inda Tinubu ya ci.
BBC ta tabbatar da sahihancin wasu daga cikin waɗannan hotunan bidiyo, yayin da kuma wakilanta suka je wasu rumfuna a Legs da 'yan daba suka hana zaɓen.
Barry Andrews, wanda shi ne mai sanya ido na Tarayyar Turai ya shaida wa BBC an samu wasu matsaloli a cikin zaɓen.
"A fili muka riƙa ganin yadda ake sayen ƙuri'u a yayin zaɓen, amma ya yi wuri mu faɗi girman matsalar yanzu," in ji shi.
Haka kuma an samu jinkirin ɗora sakamakon zaɓen, in ji shi "an samu jinkirin tsakanin zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa a wajen ɗora sakamakonsu."
BBC ta yi bincike kan wasu matsaloli biyu a kafafen sada zumunta.
A wani bidiyo da aka riƙa aikewa da shi a kafafen sada zumunta, wani ya riƙa bin shafin INEC domin bibiyar sakamakon daga Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.
Wani hoto da aka ɗauka a wannan rumfar ya kamata ya nuna sa hannun wani wakili. Maimakon hoton wata mata da ke kallon fuskar BVAS.
Kazalika BBC ta gano yadda aka riƙa cakuɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a wasu daga cikin jihohi 36 na Najeriya. Misali, an wallafa sakamakon zaɓe daga Sokoto a arewaci a matsayin sakamakon zaɓen da aka ce daga rumfar zaɓe ne a jihar Rivers da ke kudanci.
Atiku ne ya yi nasara a Sokoto yayin da Tinubu ya ci Rivers wadda aka yi tsammanin Obi ne zai yi galaba a can.
An wallafa sakamakon da ba daidai ba, kamar yadda BBC ta gano, kuma hakan ya sauya sakamakon zaɓe a wasu jihohin da dama.
Da yawa magoya bayan Obi sun yi watsi da sakamakon zaɓen da cewa an yi abin kunya.
Wannan ne zaɓen da aka fafata sosai tun bayan mayar da ƙasar kan dumukuraɗiyya a 1999.
Bayan da a ranar Alhamis biyu ga watan Fabarairu, manyan jam'iyyun hamayya biyu, PDP da LP da 'yan takararsu suka shigar da ƙara daban-daban a gaban kotun ɗaukaka ƙara a Abuja kan kotun ta ba su damar karɓar kayan da aka yi zaɓen da su, a ranar Juma'a 03 ga wata kotun ta ba su wannan dama.
A hukuncin kotun ta umarci INEC, ta bai wa kowanne daga cikinsu kayayyakin ya duba. Sannan kuma ta ba su damar titsiye hukumar zaɓen domin samun wasu bayanai.
Wannan dai na zaman wani mataki ne na sharar fagen shigar da ƙara kan zaɓen daga ɓangaren su 'yan hamayya. A martaninta jam'iyya mai mulki wadda ɗan takararta ya yi nasara ta ce a shirye take su haɗu a kotu.