Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Najeriya 2023: Jennifer Efidi, yadda aka ji min ciwo a fuska a wajen zaɓe
"Na je rumfar zaɓena, na tarar da dogon layi, ni ma na shiga layin, na ga sunana. Sai na koma gefe na zauna ina jira a zo kai na. Kawai sai na ji ƙarar bindiga."
Yadda Madam Jennifer Efidi ta yi bayani ke nan kan abin da ya faru da ita lokacin da ta je zaɓen shugaban ƙasa da na majlisar dokoki a ranar Asabar.
Hotunan Madam Bina jennifer Efidi da idonta ɗaya a toshe da kuma ɗinki a fuskarta a rumfar da ta yi zaɓe a Legas, lokacin da take kaɗa ƙuri'arta sun karaɗe kafofin sada zumunta a ƙarshen mako.
Mutane da dama sun rinƙa jinjina wa kwarin gwiwarta da jajircewarta kan yadda ta koma domin kaɗa ƙuri'arta duk da irin raunin da ke fuskarta.
A wannan tattaunawar da ta yi da BBC ta bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma abin da ya sa ta koma domin kaɗa ƙuri'arta duk da cewa an jikkata ta.
'Na ji ƙarar bindiga'
Efidi ta ce, ba ta taɓa zaton za ta samu kanta a cikin irin wannan yanayi ba a rumfar zaɓenta wadda ba ta da nisa da gidanta, ganin cewa a baya ba su taɓa fuskantar tashin hankali ba a mazaɓar.
"Na je mazaɓata, na samu dogon layi, don haka na shiga layin, bayan na duba sunana, sai na samu waje na zauna ina jiran layi ya zo kaina.
"Bayan wani lokaci, sai wasu yara suka zo inda muka yi layi, a lokacin ana ci gaba da zaɓe cikin lumana."
"Bayan kamar minti 30, sai na ji kamar wani abu ya daki fuskata kamar an jefe ni da wani abu. Kawai sai na ji ƙarar bindiga na tashi, na yi tunanin sun harbe ni. Jama'a sun ringa gudun ceton rai, sai na taɓa fuskata kawai sai na ji jini yana zuba a hannuna. Sai na fara ihun neman ɗauki, amma mutane guduwa kawai suke yi suna ta kan su.
"A haka na rarrafa na shiga wani gida, daga baya wata mata maƙociyata ce ta zo ta taimake ni. Ta samo wani ƙyalle ta ɗaure inda jinin ke zuba, muka ci gaba da kururuwar neman taimako, amma mutane suna ta kansu, suna shigewa gidajensu suna kulle ƙofa.
Daga baya sai na shiga ɗakin matar, suka ce in kira mijina, to amma sai na ji tsoron ka da su yi wa mijina illa tun da har a lokacin yaran suna nan. Sai matar gidan ta ɗauke ni muka shiga wani gidan, mutane sun yi ta ƙoƙarin tsayar da jinin. Daga baya wasu mutane suka kai ni wajen wata malamar jinya wadda ta tsayar da zubar jinin."
Efidi ta ƙara da cewa yawan jinin da ta zuɓar ya sa ta yi rauni sosai, daga baya ne kuma mijinta ya ɗauke ta zuwa asibiti domin samun cikakkiyar kulawa.
A can ne aka yi mata ɗinki a fuska a wuraren biyar, saboda ciwon da aka ji mata yana da zurfi sosai. Kuma aka yi mata allura aka ba ta magani.
'Abin da ya sa na koma'
"Na san cewa ƙuri'ata za ta yi tasiri, kuma ina so in kaɗa ƙuri'ata."
Wannan ne abin da Efidi ta faɗa bayan ta koma daga asibiti domin kaɗa ƙuri'arta, da fuskarta duk ɗinki.
Ta ce a lokacin da ta fito daga gida, ta ga mutane suna ci gaba da gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Efidi ta ce abin ya ba ta mamaki domin akwai jami'an tsaro a wajen amma ba su iya yin komai ba.Abin da mutane ke cewa
Mutane da dama sun bayyana abin da Efidi ta yi a matsayin wani abin yabawa domin ta yi jarumtar komawa ta kaɗa ƙuri'arta duk da cewa ƴan daba sun yi mata ta'addanci.
Sun kuma ringa yin tir da maharan, suna yaba mata.
Efidi ta ce ta ringa samun kira daga ciki da wajen Najeriya, mutane suna jinjina mata da nuna damuwa kan halin da ta shiga.
Ta ce ko da ɗan takarar da ta jefawa ƙuri'a bai samu nasara ba, ba abin damuwa ba ne, domin wannan a hannun Ubangiji yake.
Ga saƙonnin da wasu jama'a suka wallafa a shafinsu na Tuwita game da lamarin.