Wasu 'yan Najeriya na caccakar ma'aikatan wutar lantarki kan yajin aiki

Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan Najeriya, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun harzuka sakamakon matakin da ma'aikatan wutar lantarkin kasar suka dauka na tafiya yajin aiki.
Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da safe.
Sun kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar, domin bijire wa umarnin da hukumar da ke sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta bayar ga wasu shugabannin riko domin yin jarrabawar karin girma.
A watan sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutar lantarki, Mista Joe Ajaero ya sanya wa hannu ya umarci dukkan ma'aikatan wutar lantarki su yi zanga-zanga a hedikwatar ma'aikatar wutar lantarki da rassanta da ke fadin kasar saboda umarnin cewa dole su yi "jarrabawar karin girma."
Ma'aikatan kamfanin dillancin lantarkin na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma'aikata.
Mista Ajaero ya kara da cewa matakin ya saba wa dokokin aiki kuma an dauke shi ne ba tare da dukkan masu ruwa da tsaki ba.
Sai dai daga bisani Joe Ajaero ya ce "An janye yajin aikin da aka fara na mako biyu. A wannan daren, wuta za ta dawo."
Ya bayyana haka ne bayan sun gana da Ministan Kwadago, Chris Ngige, wanda ya sha alwashin duba korafe-korafen 'yan kungiyar.
Shi ma Ministan Harkokin Lantarki Abubakar Aliyu ya ce batutuwan da ake taƙaddama a kansu na batun ɗaukar aiki ne da suke cikin hurumin shugaban ma'aikatan gwamnati na Najeriya ba ma'aikatar lantarki ba.
'Rashin sanin ya kamata'
Sai dai 'yan kasar sun yi kakkausan suka kan ma'aikatan wutar lantarkin bisa abin da suka kira rashin sanin ya kamata da rashin duba halin da kasar ke ciki na kunci.
Maudu'ai irin su #NEPA da PHCN da #electricity na cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafin Twitter ranar Laraba zuwa Alhamis.
An rika amfani da maudu'an wajen nuna irin rashin bin doka da ke faruwa a Najeriya.
Wani fitaccen mai amfani da Twitter, Dr Joe Abah, "Gaskiya ban taba ganin wata kasa da mutane za su je su kashe makunnin wutar lantarki saboda ba sa so a yi musu jarrabawar karin girma ba, kuma ba a kama su an daure su nan take ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi ma Gimba Kakanda cewa ya yi bai ga wata hikima ba a matakin da ma'aikatan wutar lantarki suka dauka na kashe makunnin wutar lantarkin kasar kawai saboda an umarce su su yi jarrabawar karin girma.
Ita kuwa Zahrah Musa ta ce kashe makunnin wutar lantarkin wani zagon-kasa ne da ma'aikatan suka kitsa ga gwamnatin Najeriya tana mai yin kira ga Shugaba Buhari ya dauki mataki a kansu "domin kuwa ba su fi karfin Najeriya ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2











