Tasirin da kananan jam'iyyu za su iya yi a zaben Najeriya na 2023

Wasu jam`iyyun siyasa a Najeriya da ake yi wa kallon kanana na ci gaba da samun karbuwa.
Jam`iyyun dai sun yunkuro da nufin karawa da manyan jam`iyyun siyasa biyu da suka yi kaka-gida a kasar, tare da samar da zabi da kuma mafita ga al`ummar kasar.
Barrister Solomon Dalung, tsohon dan jam`iyyar APC da ya sauya-sheka ya kuma zama jigo a jam`iyyar SDP, ya shaida wa BBC cewa ko kananan jam`iyyun ba su hade ba za su yi tasiri saboda `yan Najeriya `yan takara za su bai wa fifiko ba jam'iyya ba.
Solomon Dalung ya ce "Za a zabi shugaba ne bisa cancantarsa domin wadannan jam'iyyun guda biyu sun riga sun kunna wutar yaki, PDP ta ce ba maganar karba-karba ta fitar da dan takara daga arewa mutanen kudu na guna-guni.
"APC ta fitar da dan takara daga kudu, sannan ta kawo sabon salo yanzu za a hada Musulmi da Musulmi, wadansu a Kudu kuma sun ce za a zabi Kirista da Kirista, to wannan kuwa ba karamar rigima za a tayar a kasa ba,'' in ji shi.
Rahotanni daga Najeriyar dai na nuna cewa `yan takaran shugaban kasa da shugabannin kananan jam`iyyun siyasar na ci gaba da tuntubar juna, watakila da nufin hadewa ko hada-karfi wuri guda.
To sai dai kuma masana na ganin cewa da wuya kananan jam`iyyun su yi tasiri har su cimma burinsu ba tare da sun hada kai sun kuma dunkule wuri guda ba.
Farfesa Jibrin Ibrahim, masanin siyasa a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa bisa ga yadda kananan jam`iyyun ke tafiya, musamman zaman-karofin da suke yi wato kowa da inda ya sa gabansa da wuya su cimma burinsu.
Ya ce: " Dole ne kananan jam'iyyu su taru a jam'iyya guda su hada duk karfinsu don su yi yaki sosai da manyan jam'iyyun nan guda biyu."
"In dai ana so a samu ci gaba a kuma canza yadda ake yin siyasa, to ba kowacce jam'iyya bace za tace idan zabe ya zo dole ne ta fitar da shugaban kasa," a cewarsa.
Shi kuwa Khalifa Dikwa, Malami a Jami`ar Maiduguri da ke sharhi kan lamuran yau da kullum, ya shaida wa BBC cewa gamayya ba za ta yi tasiri ba sai jam`iyyun sun dunkule, kuma lokaci ya kure.
A cewarsa: "Da alama lokaci ya riga ya kure musu, kuma idan lokaci ya kure su 'yan siyasar da wuya su janye wa wani su bi shi, saboda daga karshe idan ba ay i hankali ba aka hade gaba daya to ba za su fita ba."
Karin bayani
Tun da aka fara kada gangar siyasa jam`iyyun siyasar da ake yi wa kallon kanana, irin su jam`iyyar NNPP da Labour da SDP da PRP da APGA da sauran takwarorinsu ake jin motsinsu a sassan Najeriya.
Amon su ya yi ta amsa-kuwwa a kasar musamman ma a dan tsakanin nan, wato lokacin da aka fara gudanar da zabukan fitar da gwani, inda wasu `yan siyasa daga manyan jam`iyyu biyu da suka yi babakere a siyasar Najeriya, wato APC da PDP, wadanda suka fusata da mugun-riko ko rashin adalcin da suke zargin jam`iyyun sun musu suka yi ta sauya sheka zuwa kananan jam`iyyun.











