APC 2023: Abu biyar mafi jan hankali da suka faru a zaɓen fitar da gwani
Komai ya yi farko zai yi ƙarshe. An kammala zaɓen fitar da gwani na ƴan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyya mai mulki ta APC.
Sai dai zaɓen ya tafi ya bar ƴan ƙasar da tattauna muhimman abubuwan da suka faru.
A wannan maƙala za mu yi duba kan wasu abubuwa biyar da suka fi ɗaukar hankali a taron.
Jawaban da suka dau hankali

Bayan buɗe taro da taken ƙasa da kuma gabatar da shagulgulan yi wa baƙi maraba, sai aka bai wa ƴan takara damar yin jawaban gabatar da kansu da manufofinsa.
Ƴan takara 22 ne suka yi jawabi daga cikin 23 da suka bayyana aniyarsu.
Amma jawaban mutum shida ne suka fi jan hankali har ma suka dinga tashe a shafukan sada zumunta cikin daren.
1. Ogbonnaya Onu - an ambaci sunansa sau 23,000 a Facebook sau kusan 15,000 a tuwita
Tsohon ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu ya yi magana ne a kan yadda ba a yi wa 'yan kabilar Igbo adalci a tsarin siyasar Najeriya.
"Ba a yi wa yankin kudu maso gabas adalci. Ina adalcin yake? Ana nuna mana wariya," in ji shi.
A karshe dan takarar ya ce ba zai janye wa kowa ba kuma za a ci gaba da fafatawa da shi.
2. Rochas Okorocha - an ambaci sunansa sau 25,800 sau 32,000 a Facebook
Shi ma tsohon gwamnan Jihar Imo Sanata Rochas Okorocha kalamansa sun ja hankalin mutane, musamman a lokacin da ya saka Hausa a ciki.
Ya soki sauran masu neman takara a jam'iyyar APC cewa ba su san matsalar arewacin ƙasar ba.
"Ku tambaye su me suka yi muku...ni Rochas ɗan jikan Sokoto, ni ne na san matsalar Arewa. Wallahi billahillazi babu wanda ya kai ni son Najeriya da arewa a cikinsu" in ji Rochas kamar yadda ya fada cikin harshen Hausa.

Karin labaran da za ku so

3. Fasto Tunde Bakare - an ambaci sunansa fiye da sau 30,000 a Tuwita, sau 25,000 a Facebook
Fasto Tunde Bakare ma ya sha tashe a Tuwita, bayan da ya daddage yana faɗin yadda bai shiga neman takarar shugaban ƙasa a APC don ya janye wa wani ba.
"Da yawa daga cikin waɗannan 'yan takarar suna da matsala da hukumar EFCC," a cewarsa.
4. Ben Ayade - an ambaci sunansa fiye da sau 10,000 a Tuwita, sau 27,000 a Facebook
Shi ma gwamnan jihar Cross River ya ja hankalin jama'a da jawabansa.
Ba komai ya birge waɗanda suka dinga tataunawa akansa ba sai irin yadda ya dinga ɓarin manya-manyan kalmomin Turanci wajen bayyana irin ayyukan da ya yi a jiharsa a matsayin gwamna da kuma waɗanda zai yi a Najeriya idan ya yi nasara.
Sannan wataƙila nutsuwarsa da yadda yake jero kalamai reras sun sake burge mutane.
5. Jack Rich - an ambaci sunansa fiye da sau 14,000 a Tuwita
Jack Rich ya sha zolaya a Tuwita musamman kan labarin mahaifiyarsa da ya bayar na cewa ta sha wuya a zamanin ƴan matancinta kafin haihuwarsa.
Mutane cikin raha suke ta cewa me zai sa ya je dandalin kamfe da irin wannan batun. Sannan an dinga zolayar salon maganarsa cikin Turanci irin na Amurka.
6. Yahaya Bello an ambaci sunansa kusan sau 110,000 a Facebook sau fiye da 50,000 a tuwita
Masu amfani da shafukan sa da zumunta na ganin matashin ɗan takarar ya yi kirari ya kuma daɓawa cikinsa wuƙa - bayan da ya ce ana kashe mutane amma ba a ɗaukar mataki, sai kuma ya ɓige da cewa zai dasa daga irin abin da Shugaba Buhari ya bari.
7. Sauran waɗanda suka yi tashe a shafukan sada zumuntar sun haɗa da Bola Tinubu da Farfesa Yemi Osinbajo da Godswill Akpabio da kuma uban gayyar wato Shugaba Buhari.

Emeka Nwajiuba ya yi ɓatan dabo

Asalin hoton, Facebook Emeka Nwajiuba
Emeka Nwajiuba ƙaramin ministan ilimi ne a gwamnatin Buhari, wanda ya sauka a watan da ya gabata don tsaya wa takarar shugaban ƙasa.
Sai dai har taro ya ci ya watse babu amo babu labarin inda ya yi aure ya tare.
An yi ta ƙwalla kiran sunansa don ya fita ya gabatar da jawabi kamar yadda sauran ƴan takara ke yi, amma sai aka ji shiru, alamun ba ya wajen.
Wannan abu ya zama wani mafi jan hankali da kuma ban mamaki a taron -- musamman ganin takanas ya bar muƙaminsa don ya tsaya takarar.
Sai dai jaridar Business Day ta ruwaito cewa a cikin daren taron wani ƙaninsa ya fitar da sanarwa cewa Nwajiuba ya ƙi zuwa wajen ne saboda cin amanarsa da shugabancin jam'iyyar APC ya yi.
"Abu ne mai sauƙi. Abin da ya fahimta game da tsarin tun kafin ya tsaya takarar da kuma a matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC shi ne cewa matsaya za a cimma ta tsayar da ɗan takara kamar yadda aka yi lokacin zaɓen shugaban jam'iyya a watannin da suka gabata.
"A fahimtarsa, yankin kudancin ƙasar za a bai wa takara, musamman ma yankin kudu maso gabas," a cewar sanarwar.
A cewar ƙanin Nwajiuba yayan nasa bai yarda da ɓarin kuɗi don neman takara ba.

Janyewa Tinubu a jejjere

Asalin hoton, Jubril A Gawat
Taro ya ruɗe da sowa a daidai lokacin da ɗaya bayan ɗaya aka dinga samun masu sanar da janyewarsu daga takarar, suna umartar magoya bayansu cikin daliget da su kaɗa ƙuri'unsu ga Asiwaju Bola Tinubu.
Masu neman jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa bakwai ne suka janye tare da mara wa Bola Ahmed Tinubu baya.
Yayin da shi kuma ɗan takara Mista Nicholas Felix ya janye don mara wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo baya.
Hakan ya sa ƴan takara 14 ne suka rage a takarar daga cikin 23 da jam'iyyar ta tantance tun farko.

Rabon askirim da gugguru na Osinbajo
Wani abu da shi ma ya zama na tattaunawa a kafafen sada zumunta shi ne yadda aka dinga rabon abin sanyaya makoshi wato askirim da kuma gugguru.
Waɗannan kayayyakin suna ɗauke ne da suna da hoton mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo.
Ai kuwa hakan ce ta sa aka shiga sharhi daban-daban, ciki har da cewa wataƙila an yi hakan ne don mayar da martani kan abin da tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya faɗa kwana biyu kafin taron.
Da aka tambaye shi ko yaya zai kwatanta Farfesa Osinbajo a wata hira da Shettima ya yi da gidan talabijin na Channels TV, sai ya ce "mutumin kirki ne amma sayar da askirim da gugguru ne ya dace da shi."
Shi ya sa ake ganin rabon wadannan kayan ƙwalam da magoya bayan mataimakin shugaban ƙasar suka yi a wajen, tamkar mayar da martani ne ga Shettima, duk da cewa dai shi ma ya bayar da haƙuri kwana guda bayan "katoɓarar."

Taro ya tashi
Burin duk wani wanda ya shirya taro musamman na ɗumbin jama'a irin wannan, to babban burinsa shi ne a kammala shi lafiya babu kun ji-kun jin da za su ɗaga hankali.
An ɗauki lokaci ana ƙirga ƙuri'a inda daga bayar aka sanar da Asiwaju Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Sannan an bai wa Tinubu dama ya yi jawabi a kan manufofinsa a matsayin ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen 2023.
A lokacin da yake jawabin, an ga matarsa a gefensa har ta raka shi kan dandamalin bayanin, kuma an lura da yadda take kaffa-kaffa da shi.
A ƙarshen hidimar kuma an kira shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban jam'iyya Abdullahi Adamu inda aka ba shi tutar jam'iyya a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2023.












