Zaben 2023: Abin da 'yan Najeriya suke cewa game da ƙurar da Tinubu ya tayar a jam'iyyar APC

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/ Bola Ahmed Tinubu

Bayanan hoto, Tinubu ya ce Buhari ya nemi ya yi masa mataimaki a zaɓen 2015
Lokacin karatu: Minti 4

Bugun ƙirjin da tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ya yi cewa "ba don ni ba da Muhammadu Buhari bai zama shugaban ƙasa ba" ya tayar da kura a kasar tare da haddasa muhawara da bayyana mabambantan ra'ayoyi a ciki da wajen kasar.

"Tun da ya zama shugaban ƙasa ban taɓa samun wasu kwangiloli ba, ban taɓa samun kujerar minista ba, ban taɓa roƙar sa komai ba, amma fa ina faɗa cewa lokacin Yarabawa ne...ni ma ina so na zama shugaban ƙasa," in ji Tinubu yayin kamfen din da ya je yi a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun ranar Alhamis.

Yayin jawabinsa, Tinubu ya roƙi wakilai masu jefa ƙuri'a wato daliget da su mara masa baya, kada su mayar da zaɓen a matsayin "ƙabilanci" yayin da ya rage kwana uku kacal jam'iyyarsu ta APC mai mulkin kasar ta gudanar da zaɓen fitar da gwani.

'Yan takara fiye da 20 ne ke neman a ba su takarar, ciki har a Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo - wanda Tinubu ya ce shi ne ya ba da sunan sa a matsayin mataimakin Buhari - ɗan ƙabilar Yarabawa kuma daga yankin kudu maso yamma kamar Tinubu.

Wani ɗan jarida mai suna Taiwo Alabi (@taiwoalabiho2) ya faɗa cikin raha a shafinsa na Twitter cewa: "Na zaci muna ta zargin Tinubu ne saboda ya kawo Buhari? Yanzu ya faɗa cewa shi ne ya kawo shi amma kuna musantawa."

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A Facebook ma, Umar Musa Matazu cewa ya yi "wasan fa ya fara zafi, har an fara sauya harshe ana yi wa Buhari gori".

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

'Ba don ni ba da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba'

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Jagoran na APC ya ce ƙawancen da ya ƙulla da Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ne ya sa ya ci zaɓe bayan ya faɗi har sau uku.

"Shugabancin ƙasa ba na Arewa ba ne kaɗai," in ji Tinubu. "Ba don ni ba da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba. Ya faɗi a karon farko ya faɗi a karo na biyu, ya faɗi a karo na uku. Har ma ya fashe da kuka a talabijin yana cewa ba zai sake neman takara ba.

"Amma na haɗu da shi a Kaduna, na ce ya sake nema kuma da taimakona zai yi nasara amma [da sharaɗin] ba zai yi raina wa Yarabawa wayo ba, kuma ya amince.

"Tunda ya zama shugaban ƙasa ban taɓa samun wasu kwangiloli ba, ban taɓa samun kujerar minista ba, ban taɓa roƙar sa komai ba, amma fa ina faɗa cewa lokacina ya yi...ni ma ina so na zama shugaban ƙasa, amma ina jaddada cewa lokacin Yarabawa ya yi. Hatta a loakcin ma lokacina ne."

Na gaji da taimakon mutane, ina so na zama shugaban ƙasa ni ma - Tinubu

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Yayin jawabin na jagoran APC, Tinubu ya taɓo abubua da dama, ciki har da kiran sunayen mutanen da ya taimaka a siyasa tsawon lokaci, kamar Atiku Abubakar ɗan takarar PDP, da Gwamnan Ogun Dapo Abiodun, da Yemi Osinbajo da Shugaba Buhari kansa.

"Loƙacin da aka fitar da Atiku daga PDP, wajena ya zo neman taimako. Haka ma Nuhu Ribadu, wajena ya zo na taimaka masa.

"Sama da shekara 25 ke nan ina taimaka musu.

"Hatta Gwmana Abiodun da ke zaune a nan; zai ce ya zama gwamna ne ba tare da taimakona ba? Ya san ba zai iya zama gwamna ba ba tare da ikon Allah da kuma taimakona ba."

Ya ƙara da cewa: "Ku ba ni shugaban ƙasa, loƙacina ne...Na gaji da taimakon mutane, ina so na zama shugaban ƙasa ni ma."

Rabuwar kai kan mutumin da Buhari yake son ya gaje shi a APC

Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Bayanan hoto, Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar (hagu) na cikin 'yan takarar da rahotanni ke cewa yana da goshi a fadar shugaban ƙasa

Rahotanni na nuna an samu rabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan APC kan mutumin da Shugaba Buhari ke son zaɓa domin ya gaje shi a inuwar jam'iyyar.

A ranar Laraba mataimakin shugaban jam'iyyar na reshen arewa maso yamma, Mallam Salihu Lukman, ya aike da wata buɗaɗɗiyar wasika da ke gargaɗin cewa zaɓin Buhari na iya haifar da barazana ga jam'iyyar da shugabancinta.

Akwai kuma wasu rahotanni da ke nuna cewa ba a iya cimma matsaya a taron da gwamnonin suka yi a daren Talata kan yin neman fitar da ɗan takara ta hanyar sasantawa, wanda Buhari ke so.

Gwamnoni da dama na APC na da ra'ayin cewa ya kamata mulki ya koma kudancin Najeriya, cikinsu har da Nasir El-Rufai na Kaduna, da Gwamna Babagana Zulum na Borno, da Abdullahi Ganduje na Kano.

A ranar Talata da ta gabata APC ta tantance masu neman takarar shugaban kasar, waɗanda suka zarce mutum 20.

'Yan Najeriya na dako domin sanin wanda APC za ta tsayar don fafatawa da sauran 'yan takara na jam'iyyu musamman Atiku Abubakar na wanda babbar jam'iyyar Adawa ta PDP ta zaɓa a matsayin ɗan takararta.