Kasuwar 'yan kwallo: Makomar, Haaland, Sterling, De Jong, Eriksen, Salah, Jones, Zinchenko

Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Bayan da ta kasa daukar Kylian Mbappe, Real Madrid na shirin biyan yuro miliyan 150 domin daukar sabon dan wasan Manchester City Erling Haaland idan yana son barin Etihad kafin wa'adin kwangilarsa ya kare a 2024. (AS)

Chelsea na son sayen dan kwallon Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27. (Fabrizio Romano, via Express)

Manchester United na fatan Barcelona za ta rage farashin fam miliyan 80 da ta sanya kan dan wasa mai shekara 25 dan kwallon Netherlands, Frenkie de Jong. (Athletic, subscription required)

Kociyan Manchester United, Erik ten Hag, ya bukaci masu kungiyar su sayo masa De Jong, da kuma dan kwallon Denmark, Christian Eriksen, mai shekara 30, domin da su zai gina kungiyar. (Mirror)

Liverpool na fargabar rabuwa da dan kwallon tawagar Masar, Mohamed Salah, mai shekara 30, a badi a araha, bayan da ba su amince da albashin fam 400,000 duk mako da ya bukata ba. (Mirror)

Mai tsaron bayan Manchester United, Phil Jones, mai shekara 30, yana daga cikin jerin 'yan wasan da Leeds United, ke son dauka, sai dai Marc Cucurella, 23. (Fabrizio Romano)Marc Cucurella, 23. (Fabrizio Romano)kuma Southampton da Fulham na son yin zawarcin dan kwallon Ingila. (Marca - in Spanish)

Manchester City za ta bar Oleksandr Zinchenko, mai shekara 25, ya bar kungiyar - Everton ce ke son daukar dan kwallon - City na shirin taya dan wasan Brighton, Marc Cucurella.(Fabrizio Romano)

Brighton na bukatar fam miliyan 50 kudin Cucurella, wannan farashin ka iya sa City ta hakura da cinikin dan kwallon. (Athletic, subscription required)

Liverpool ta sanar da mai sharon baya, Neco Williams, mai shekara 21 za ta bayar da aronsa kafin fara kakar bana, yayin da Nottingham Forest ke sha'ar dan kwallon Wales din. (Mirror)

Ajax ta ki sallama tayin fam miliyan 25 a daga Arsenal da ta yi wa mai shekara 24 dan kasar Argentina mai tsaron baya Lisandro Martinez. (Mail)

Brighton da Watford na rige-rige a kokarin daukar dan kwallon Olympiakos mai shekara 27 mai tsaron bayan tawagar Senegal, Pape Abou Cisse. (Star)

Millwall ta yi wa Aberdeen £1.5m ta yin fam miliyan daya da rabi ga dan wasan Scotland, Lewis Ferguson, mai shekara 22, tana kuma son daukar aron dan wasan Stoke, Benik Afobe, mai shekara 29 . (Telegraph)