Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karancin dalar Amurka na kokarin durkusar da masana'antu a Najeriya
Kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya sun koka kan yadda ba sa iya samun dalar Amurka daga babban bankin kasar don shigo da hajoji a daidai lokacin da farashinta ya tashi a kasuwar bayan-fage.
Kungiyar masu masana'antun ta ce sun dade suna kokawa ga gwamnati kan yadda tashin dalar da karancinta yake shafar kasuwancinsu, amma ba a yi komai kan hakan ba.
Masu masana'antu na wannan furuci ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar farashin kayan masarufi tare da tashin farashin dala a kasuwannin bayan-fage da ke kasar.
Alhaji Aliyu Sufyanu Madugu, mataimakin shugaban kungiyar masana'antu masu zaman kansu a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa rashin samun dalar Amurka yana gab da durkusar da masana'antunsu, sakamakon yadda ba sa iya samar da kayayyakin da suka dace.
Ya ce: ''Ba wai tashin farashin dala kadai ake magana anan ba, a'a babu dalar ce ma baki daya, duk wanda ya ke da masana'anta a Najeriya ya ke sarrafa wani abu, ya kuma ke kawo kayan aiki daga waje, ko na gyara ya na cikin matsanancin hali.
Mu da muke da kamfanoni a Najeriya, mu na yin bidding a babban bankin Najeriya wato CBN, amman abin damuwar shi ne kai da ka ke neman $100,000 a sati, sai ka yi sati biyu har zuwa uku ba ka samu ko da $2000 ko $3000 ba.
Idan da za ka iya zuwa ka saya abayan fage ka same ta ma da sauki, to nan din ba babu wani sauki, sai dai wai idan wani ya sayar da kaya a waje ya samu dalar ka bi shi ka saya, nan din ma babu tabbas.
Ta yaya za ka gudanar da aikin ka? ta yaya za ka biya ma'aikatan da ake karkashin ka tun da ka samar da abubuwan da ake bukata wajen yin kayan ba, wanda sai an saida su sannan za ka biya ma'aikata, maganar gaskiya mu na cikin mummunan yanayi,'' in ji shi Ali Sufyanu Madugu.
Tashin farashin dalar Amurkar dai ya janyo tashin farashin kayayyaki musamman ma masarufi a Najeriyar, ya yin da karancin ba da ita daga bankuna da su kuma suke samu daga babban bankin Najeriyar ke kara janyo kunci ga wadanda suka dogara da ita domin hada-hadar kasuwanci.
Masana na ganin cewa za a iya magance matsalar rashin ayyukan yi da ake fama da ita, musamman tsakanin matasa, inda masana'antun da ake da su a fadin kasar na aiki yadda ya dace.