Tasirin Coronavirus: Dokar kulle 'ta durƙusar da ƙananan masana'antun arewacin Najeriya'

Dokar kullen da gwamnatin Najeriya ta sanya da zummar daƙaile yaɗuwar cutar korona ta durƙusar da ƙananan masana'antun arewacin Najeriya.

Dr Dikko Umaru Radda, shugaban hukumar bunƙasa matsakaita da ƙananan masana'antun ƙasar ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da BBC Hausa.

Sai dai ya ce akwai tsarin tallafi da kuma rancen da Babban Bankin ƙasar ke bayarwa waɗanda za su taimaka wa masu ƙananan sana'oi.

"Babban ciwon ƙanana da matsakaitan masana'antu na ƙasar nan idan ka tambaye su shi ne, rashin samun kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukansu. Kuma an fito da wani shiri wanda Babban Bankin ƙasar ya samar wanda ake ba da tallafin naira miliyan ɗaya zuwa miliyan 10.

"Abin da kake buƙata ka je hukumar da ke horar da ƙananan da matsakaitan masana'antu a tabbatar da an horar da kai, wannan takarda ta horarwa ita ce babban ginshiƙi na wannan bashin da za a ba ka," in ji shi.

A cewarsa, cutar korona ta shafi tattalin arzikin duniya musamman a Najeriya da kusan mutum miliyan 60 na 'yan kasar sun dogara ne kan kananan da matsakaitan sana'oi.

Ya ce: "A Najeriya, muna da kusan mutum miliyan 41,500,000 wadanda masu yin kananan da matsakaitan masana'antu ne, kuma abin da ya mayar da Najeriya ta samu matsala, shi ne kusan wannan adadi miliyan 40 da wani abu 'yan kananan masana'antu ne wadanda jarinsu karami ne a kauyuka suke."

Ya kuma ce nnoba da ta zo ta taimaka wajen ganin cewa sun cinye jarinsu, wasu sana'arsu ta kare saboda (kulle), amma kusan tallafin da gwamnati ke fito da su za ka ga ana kallon kanana da matsakaitan masana'antu, wadanda za ka su ba sa ma da abin da za su iya zuwa banki su iya samun wadannan basussukan da gwamnati ta ke, ba a basu mahimmanci kamar yadda ya kamata.

A ganinsa, irin wadannan masu karamin karfi ba bashi ya kamata a basu ba, "tallafi ya kamata a basu daga naira dubu 10 zuwa dubu 50 har 100 dai-dai gwargwadon irin abin da kake, ba karamin taimakawa zai yi ba."

Ya ce sun ba da shawarwari ga wani kwamiti da ke karkashin mataimakin shugaban kasa na ganin yadda a kowace karamar hukuma, "an dauki masu irin kananan sana'oi kusan dari 500 a kananan hukumomi 774 a basu tallafin ko da dubu 50 ne don ganin cewa sun bunkasa tattalin arzikinsu kuma mafi yawan wadannan mutane suna arewacin Najeriya."

'An bar arewa a baya'

Dr Radda ya ce akwai bukatar mutanen arewa su shiga irin wannan tsari saboda "daga sanda aka fara wannan abun, idan ka kalli mutanen da suka amfana, da wadannan kudade za ka ga mafi yawanci mutanen kudancin Najeriya ne.

Acewar sa hakan ta na faruwa ne "saboda su suna da dagewa wajen bin diddigin irin wadannan tallafi da gwamnati take badawa da ganin cewa kuma abubuwan sun kai."

Mafita

Shugaban hukumar ta bunkasa matsakaita da kananan masana'antu a Najeriyar ya ce ya kamata al'ummar arewa su jajirce "yadda kowa yake dagewa yana neman abin nan suma su jajirce su neme shi."

"Kuma duk wuraren nan, mu hukumarmu abin da muke muna ta fadakar da mutane, yanzu haka akwai shirin da muke gidan rediyo da talbijin da kuma yarurruka kala-kala na (fadawa) mutanen Najeriya cewa akwai kaza a wuri kaza yana da kyau kuje wuri kaza" don samun moriyar shirin", in ji Dr Radda.