Kungiyar Opec: Me ya sa kasashe mafi karfin arzikin man fetur suka ki rage farashinsa?

Asalin hoton, Getty Images
Manyan kasashen da ke samar da man fetur a duniya za su tattauna a ranar biyar ga watan Mayu, bayan kiraye-kirayen da ake yi musu na sauko da farashin danyen man fetur.
Farashin dayen man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba cikin shekara takwas kuma kasashen masu sayen man na son kungiyar Opec+ ta kara yawan man da take hakowa.
Sai dai manyan kasashen da ke cikin kungiyar ba sa rububin taimakawa.
Me ake nufi da Opec+?
Opec+ wata kungiya ce ta kasashe 23 masu arzikin man fetur da ke ganawa a kowane wata a birnin Vienna domin yanke hukunci kan yawan man fetur din da za su shigar cikin kasuwar duniya.
A tsakiyar wannan kungiyar akwai kasashe 13 na kungiyar Opec, wadanda akasari kasashen Gabas ta Tsakiya da Afirka ne. An kafa ta ne a 1960 domin magance matsalar karancin man fetur da farashinsa.
A 'yan shekarun nan, kasashen kungiyar Opec na samar da kimanin kashi 30 cikin 100 na dukan danyen man fetur din da duniya ke bukata, wanda ya kai ganga miliyan 28 a kowace rana.
Kasar da tafi fitar da danyen ma fetur cikin wadannan kasashen ita ce Saudiyya, inda take samar da ganga miliyan 10 ta danyen man fetur a kowace rana.
A shekarar 2016, yayin da farashin man fetur ya ragu sosai, Opec ta hada kai da wasu kasashe 10 da ba sa cikin kungiyar domin kafa sabuar kungiya mai suna Opec+.

Kasar da ta fi muhimanci cikin sababbin kasashen ita ce Rasha, wadda ke samar da gangar danyen mai miliyan 10 cikin kowace rana.
Idan aka hada alkaluma, wadannan kasashen na samar da kimanin kashi 40 cikin 100 na danyen man fetur da duniya ke bukata.
"Opec+ na samar da mai daidai da bukatun kasuwa ne", in ji Kate Dourian ta cibiyar Energy Institute.
"Su kan rage yawan man ne domin farashi ya tashi da zarar sun gano kasuwa ta fadi."
Sai dai Opec+ na da ikon rage farashin man ta hanyar kara yawan man da suke hakowa, wanda shi ne abin da kasashe masu sayen man kamar Amurka da Birtaniya ke son ganin an yi.

Me ya janyo tashin farashin man fetur sosai haka?
A shekarar 2020 yayin da annobar korona ke kara yaduwa, kuma an kulle al'umomin kasashe duniya a gida, farashin man fetur ya fadi warwas saboda rashin masu bukatarsa.
A sanadin haka ne dukkan kasashen kungiyar Opec+ suka amince su rage yawan man da suke hakowa da ganga miliyan 10 a kowace rana domin su farfado da farashin man a kasuwa.
A watan Yunin 2021, lokacin da kasuwar man fetur ta fara farfadowa, sai Opec+ ta kara yawan man da ta ke fitarwa sannu a hankali daga wata zuwa wata, lamarin da yasa ta karo ganga 400,000 cikin kasuwar duniya a kowace rana.
A yau tana samar da ganga miliyan biyu da rabi a kowace rana kasa da yadda ta saba samarwa a shekarar 2020.
Amma bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, farashin ya yi tashin goron zabi zuwa dalar Amurka 100 kan kowace ganga daya ta anyen man fetur. Wannan ne yasa farashin man ya tashi sosai har a gidajen mai na kasashen duniya.
"Lokacin da Opec+ ta rage ganga miliyan 10 a kowace rana a 2020, sun yi ragi mai matukar yawa," in ji David Fyfe, na kamfanin Argus Media.
"Yanzu suna kara yawan man sannu a hankali, wanda ba ya la'akari da tasirin yakin da Rasha ke yi a Ukraine.
Akwai masu fargabar cewa tarayyar Turai za t bi sahun Amurka domin kakaba mata takunkumi kan sayen man fetur dinta, in ji Mista Fyfe. A halin yanzu Turai na shigar da gangar danyen mai miliyan biyu da rabi a kowace rana daga Rasha.
"Fargabar daina sayen mai daga Rasha ya tsorata kasuwannin duniya," in ji shi "saboda matakin ka iya haifar da matsanancin karancin man a duniya."
Me ya sa Opec+ ta ki kara yawan ma da ta ke fitarwa?
Shugaba Joe Biden na Amurka ya sha yin kira ga Saudiyya ta kara yawan man da take fitarwa amma a banza.
Firaministan Birtaniya ma ya bukaci Saudiyyar da Hadaddiayar Daular Larabawa da su kara yawan man da suke kai wa kasuwannin duniya, bukatar da ya bayyana yayin da ya kai wata ziyarar aiki zuwa kasashen biyu. Shi ma an yi banza da shi.

Asalin hoton, Gertty Images
"Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa na iya kara yawan man da suke hakowa, amma sun ki yi haka ne domin kashin kansu," inji Kate Dourian. "Ba sa son kasashen yamma su rika gaya musu abin da za su yi."
Sauran mambobin kungiyar Opec+ ma na fuskantar kalubale wajen kara yawan man da suke hakowa.
David Fyfe ya ce "Cikin shekara da ta gabata, kasashe kamar Najeriya da Angola suna rage yaan danyen man da aka amince musu su hako a kowace rana da ganga miliyan daya."
Mece ce matsayar Rasha?
Kungiyar Opec+ ma ta mutunta bukatun Rasha, tun da tana daya daga cikin manyan kasashe biyu da ke cikin kungiyar.
"Rashawa na murna da yadda kasuwar mai take a halin yanzu," kamar yadda Carole Nakhle ta kamfanin samar da makamashi na Crystol Energy ke cewa. "Ba su da asara idan farashin ya ci gaba da zama yadda yake a yanzu".










