Abin da ya sa sojojin Myanmar suke guduwa daga aiki

Agne Lay with three fingers up in front of his face, a symbol of resistance
Bayanan hoto, Agne Lay na ishara da hannuwansa domin nuna goyon bayansa ga gwamnatin farar-hula
    • Marubuci, Daga Reha Kansara
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Trending

Matsalar yakin-basasa ta dabaibaye Myanmar, wadda ta fara tun lokacin sojojin Tatmadaw - wadanda suka kwace mulki a bara. Yanzu wata tawagar sojoji da ke da zaure a Facebook da Telegram na taimaka wa sojojin da ke son guduwa su bar aiki.

Agne Lay - ba sunansa ba ne na gaskiya - yana zaune a gefen wayarsa yana jira a kira shi.

Bayan minti biyar sai ya samu sakon kar-ta-kwana.

Wani soji cikin dimuwa na bukatar taimakonsa. Yana son barin rundunar Tatmadaw, amma yana fargabar kada a kama shi. Ko Lay zai iya taimaka masa?

Kusan kowacce rana sai ya samu sakonni irin wadannan, ba ma shi ba har da sauran mutanen da suke taimako na sa-kai suna samun irin wadannan sakonnin daga sojoji da 'yan sanda masu son barin aiki.

"Mun tallata a Facebook cewa wadanda suke son barin aiki su tuntube mu ta Telegram," in ji Lay, wata harkalla da ake yi a iya intanet ba tare da fadin wurin da masu yin ta suke ba a Burma.

Yayin da Tatmawad ke ci gaba da bibiyar adireshin intanet dinsu, yana tsoron kada su gano takamaimai daga inda suke aiki. Amma na yi magana da 'yan tawagar Tatmadaw na ji yadda suke aiki.

Ayyukansu a tattare suke da hadari mai yawa. Mista Lay ya ce ya san abin da zai faru idan tsohon maigidansa ya kama shi.

"Za a kashe ni ne," a cewarsa.

Rikicin da ya kai ga asarar rayuka

Fararen hula da ke zanga-zangar neman a saki tsohuwar shugabar kasar bayan juyun mulkin da aka yi a bara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fararen-hula da ke zanga-zangar neman a saki tsohuwar shugabar kasar bayan juyin mulkin da aka yi a bara

Yakin-basasar Myanmar ya koma mummunan rikici bayan juyin-mulkin da aka yi a bara, aka hambarar da gwamnatin fararen-hula.

A ranar 1 ga watan Fabrairun 2021, bayan an saki zaban Aung San Suu Kyi, sojojin kasar sun hambarar da gwamnatin jam'iyyar NLD. Shugabannin sojoji sun kafa hujja da cewa an yi magudi a zaben, duk da cewa hukumar zabe ta kasar ta ce babu wata hujja da ke nuna hakan.

Fararen-hula sun fara zanga-zanga, sai dai sun hadu da fushin sojoji.

A wancan lokacin, Lay soja ne kuma a ofis yake zaune yake aiki. Ya rude da rikicin da ke faruwa, don haka sai ya koma kafafen sada zumunta domin nemo tafita. Ya ce sai ya ga yadda sojoji ke yi wa fararen-hula kisan-azarbabi.

"Na ga yadda aka rika kai wa mutane hari da gayya, ana harbinsu a ka ana kashe su," in ji shi. "Babu kisan da aka yi bisa kuskure."

Abin ya kara munana ne a gare shi, lokacin da ya ga sojojin sun tilasta wa dansa mai shekara 13 shiga soji - a wannan lokacin babu abin da zai iya yi domin dakatar da su.

"An gaya mani cewa idan na yi kokarin dakatar da su, za a hukunta ni," in ji Lay.

Shi ne karshen tashin hankali ke nan.

"Ba na fatan ci gaba da zama soja," ya ce.

Wata biyar bayan wannan juyin mulki, Lay ya tattara iyalansa sun koma cikin duwatsu da zama. Su ne rukunin farko da mutane suka taimakawa.

Dubban fararen hula ne suka yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin soji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban fararen hula ne suka yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin soji

Amfani da intanet a matsayin makami.

Lay na cikin wadanda suke shirya komai. Yana aiki daga wani boyayyen waje - a yankunan da 'yan tawayen ke da iko da su, Inda mutanen da ba su da rinjaye ke da yawa kuma nan NUG take.

Ya yi mani bayani kan yadda Facebook da Telegram suka zama hanyar sauya mutane da yadda suka ba shi damar tserewa.

Shafin nasu na da mabiya sama da 100,000. wadanda suke aikin tabbatar da mutanen da suke nemansu a intanet sun samu abin da suke so.

"Idan abokanmu na son barin soji, sai su yi ta turan adireshin shafinmu," in ji shi.

Kafafen sada zumunta suna matukar taka rawa wajen rubuta sabon tarihin Myanmar.

Shekara 10 baya kadan ne ke da waya ba ma maganar intanet ba.

Tawagarsa ta tantance bidiyoyi masu yawa da ake rika sanya wa a intanet suna nuna sojoji suna cin zarafin mutane.

Facebook kuma wani wuri ne da ake amfani da shi wajen yada labaran karya da yada tsana tsakanin mutane. Wannan ne ya janyo kisan kare dangin da aka yi wa musulman Rohingya kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, ya kuma kara da cewa manyan sojojin Myanmar na bukatar a bincike su kan wannan abin da ya faru a jihar Rakhine. Amma a lokaci guda sai gwamnatin Myanmar ta yi watsi da duka zarge-zargen.

A member of the opposition uses his smartphone at base camp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mamba na 'yan adawa na amfani da wayarsa

Shi ya sa tsohon ma'aikacin MDD James Rodeheaver, ya bayyana kafafen sada zumunta a nan kasar kamar wata takobi mai baki biyu.

Sabuwar safiya

BBC ta tuntubi sojojin domin bayyana musu zarge-zargen da Lay da wasu mutane suka yi, amma har yanzu babu amsa.

Yayin da rikicin ke kara karfi, PE da NUG na kara samun goyon baya mutane.

Ba za mu iya fadin adadin ba, amma NUG ta ce sama da sojoji da 'yansada 8,000 ne suka tsere daga aiki. Wasu kuma kai tsaye suke komawa yaki da sojojin.

Da taimakon da ya yi wa mutane da yawa, Lay yana jin ya cimma wani gagarumin abu a rayuwarsa.

Ya ce zai ci gaba da wannan yaki har sai an mayar da gwamnatin fararen-hula - an hambarar da ta Tatmadaw.