Darfur: Abin da ya sa mayakan Janjaweed na Sudan suka dawo da kai hare-hare

Rapid Support Forces pictured in Darfur, Sudan in 2019

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An faɗaɗa Rundunar Agajin Gaggawa ta Janjweed (RSF) kuma wasu daga cikin mambobinta na cikin rikicin baya-bayan nan
    • Marubuci, Daga Mohanad Hashim
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

An kaddamar da hari mai muni a wani birnin da ke yankin Darfur a Sudan - kwanaki kadan bayan dubban mutane sun isa birnin domin samun mafaka sakamakon harin da mayakan Janjaweed suka kai garinsu a kan dokuna inda suka kone shi.

"A karon farko a tarihin Geneina, an kwashe kowa daga asibitin birnin. An rufe dukkan cibiyoyin kula da lafiya na birnin," kamar yadda Babban Kwamitin tlikitocin Sudan ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

Ko a lokacin da ake tsaka da rikicin Darfur wanda aka soma a 2003 - a yakin da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 300,000 sannan ya raba fiye da mutum miliyan biyu da gidajensu - asibitin Geneina da ke Yammacin Darfur ya ci gaba da aiki.

Wani ma'aikacin agaji a Geneina ya shaida wa BBC shi da abokin aikinsa sun zauna a tudun-mun-tsira kuma suna jin karar harbe-harbe a cikin birnin.

Iyalai da dama da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira da ke kudancin birnin bayan sun tsere wa mayakan Janjaweed a baya sun soma fargaba inda suka suka rika guduwa daga mazasunin wucin-gadin da suke.

Tashin hankali na baya-bayan nan ya fara ne kilomita 80 a gabas da Geneina da ke Kreinik a ranar Juma'a, kuma an kashe mutum sama da 200 a arangamar.

Me ya haifar da arangamar?

Rikicin ya faru ne sakamakon arangama tsakanin Larabawa makiyaya da kuma 'yan ƙabilar Massalit, waɗanda suka shafe shekaru suna gwabzawa kan fili.

Ya fara ne bayan kashe Larabawa biyu a kusa da Kreinik, garin da ya zama matsugunin 'yan Massalit da yawa bayan raba su da muhallansu cikin shekara 20 da suka wuce - mutanen da mayaƙan sa-kai na Janjaweed suka kora daga gidajensu.

A burnt out settlement in West Darfur - 2008

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kori mutane da dama daga gidajensu cikin shekara 20 da suka gabata

Don ɗaukar fansar kisan makiyayan, da asubahin Juma'a wasu mayaƙan Larabawa suka far wa Kreinik tare daa kashe mutum tara, suka kuma raunata 16.

Sai kuma ranar Lahadi, inda aka kai wani babban hari tare da tallafin Rundunar Agajin Gaggawa ta Sudan (RSF), wata runduna da ta samo asali daga Janjaweed.

Maharan sun iso a motoci masu majanyu huɗu (4x4) ɗauke da bindigar mashinga, da babura, da raƙuma, da kuma dawakai, in ji wata sanarwa daga ƙungiyar matasan Kreinik.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna dandazon mayaƙan Larabawa a kan motoci da babura yayin da suke kan hanyarsu ta kai hari. Ana iya ganin dakaru sanye da kakin RSF a bidiyon.

An cinna wa garin wuta kuma kafofin yaɗa labaran yankin sun ce har asibiti da makarantu ba a bari ba - malamai shida aka kashe a harin.

An hari wani asibiti da ke ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF).

"Mutum uku, ciki har da ma'aikatan lafiya biyu, aka kashe. Kazalika, an yashe wurin ajiyar magunguna na asibitin," a cewar wata sanarwar MSF.

Me ya sa jami'an tsaro ba su dakatar da maharan ba?

Tsawon shekaru, dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) na ta ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya. Amma sun janye daga yankin a 2020 bayan ƙarewar wa'adinsu - da yawa ba su so zamansu ba a yankin. Amma ko a lokacin da suke nan, ba za su iya hana wannan harin mai ƙarfi ba.

Yanzu aikin kiyayen zaman lafiya a Darfur ya koma hannun haɗin gwiwar 'yan sanda da sojoji da rundunar RSF da kuma gungun 'yan tawaye da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a 2020.

Sai dai a bayan fage - dukkansu na da buruka da suka sha bamban.

Akwai 'yan ƙabilar Massalit da yawa a cikin 'yan sanda, ita kuma RSF na da 'yan Janjaweed - waɗanda wasu daga cikinsu suke cikin faɗan na baya-bayan nan.

Dakarun da ke gadin Kreinik sun fice daga yankin kafin harin, a cewar masu fafutika na yankin.

Me ya sa faɗan ya kai har Geneina?

Mayaƙan Janjaweed da na RSF na bin sawun wasu mayaƙa ne daga Kreinik zuwa Geneina - kuma hakan ya kai ga far wa asibiti da kuma tashin hankalin da ya shafi ƙabilanci da ya ɗan lafa a baya.

1px transparent line

Geneina ne babban birnin Masarautar Massalit na gargajiya - wata alamar ƙarfin ikon baƙaƙen fata a Darfur, saboda haka Janjaweed ke baƙin cikin hakan, waɗanda ake zargi da aikata kisan ƙare-dangi a Darfur.

Rikici ya fara ɓallewa ne da farko a Darfur a 2003 lokacin da akasarin waɗanda ba Larabawa ba suka yi wa gwamnati tawaye, suna ƙorafin nuna musu wariya da kuma rashin ci gaba.

Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar bai wa Janjaweed makamai don yaƙr 'yan tawayen, inda suka ƙaddamar da rashin imanin da ya jawo ɓacin rai a faɗin duniya wanda kuma ya jawo aka tura dakarun kiyaye zaman lafiya da kuma ba da umarnin kame.

Karo na uku kenan ana kai wa Geneina hari tun daga 2019 - wani lokaci na sauyi yayin da aka tumɓuke Omar al-Bashir a matsayin shugaban ƙasa bayan kusan shekara 30.

A watan Maris na wannan shekarar, tashin hankali ya yi sanadiyyar kisan gwamman mutane da kuma ƙona ƙauyuka da dama a garin Jebel Moon da ke Geneina.

Yankin Darfur na da arzikin zinariya, kuma ana zargin 'yan Janjaweed da kai hare-hare don kame ƙarin filaye da zimmar haƙo ma'adanai.

Adam Rajal - wani mai magan da yawun gidauniyar 'yan gudun hijira ta IDPs Co-ordination Committee da ke aiki da dukkan sansanonin waɗanda aka raba da muhallansu - yana ganin yunƙuri ne na lalata sansanonin.

Tsohon shugaban Janjaweed, Ali Muhammad Ali Abd-al-Rahman da ke fuskantar shari'a a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya musanta zargin aikata laifuka kan rayuwar ɗan Adam. Shi ne mutum na farko da kotun ta ICC ke wa shari'a kan batun. Shi ma al-Bashir kotun na nemansa kan laifukan duk da ya musanta.

"Manufar ita ce a kori dukkan mutanen garuruwan kuma a lalata sansanonin...waɗannan sansanonin ne hujja mafi ƙarfi ta laifukan kisan ƙare-dangi da kisan kiyashi, da kuma laifukan da gwamnatin da ta gabata ta aikata," a cewar Mista Rajal.

Me ya sa RSF ke da ƙarfin iko?

Gwamnan yankin Darfur, Minni Minawi wanda tsohomn shugaban 'yan tawaye ne, ya zargi gwamnatin Sudan da nun ahalin ko-in-kula game da ayyukan RSF.

Sai dai rundunar da na ƙarfin iko sosai a gwamnatin sojan ƙasar, kuma shugabanta Laftanar Janar Mohamed Hamdan "Hemeti" Dagolo shi ne mataimakin shugaban Sudan.

Janar wanda Balaraben Chadi ne, ya taso a Darfur - kuma ya faɗaɗa rundunar RSF ta ƙunshi mayaƙa daga sauran sassan ƙasar.

Masu sharhi na cewa yana amfani da rikicin ƙabilancin ne don ya cimma muradin siyasarsa.

An sha zargin Janjaweed da ɗaukar mayaƙa Larabawa daga Chadi da sauran ƙasashen yankin Sahel - ta yadda ake ƙarfafa musu gwiwar zaunar da iyalansu don sauya yanayin siyasar Darfur.

Janar Hemeti bai taɓa magana kan zarge-zargen ba ko kuma tashin hankalin da ke faruwa na baya-bayan nan a Yammcin Darfur, amma ya sha kiran al'ummomin da ke Darfur ɗin su zauna lafiya a bayanan sanarwar da yake fitarwa.