Tsautsayi da riba a haramtacciyar masana'antar mai ta Najeriya

A man near burn-out vehicles after an explosion at an illegal oil refinery in the Niger Delta, Nigeria - April 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An binne mutanen da suka mutu cikin manyan ƙaburbura a gagarumin tsautsayin da ya faru a wata haramtacciyar matatar mai da ke Jihar Imo a kudancin Najeriya

Mutuwar fiye da mutum 100 sakamakon wata fashewa a wata haramtacciyar matatar man fetur a kudancin Najeriya ta haska yadda ake cin kasuwar bayan-fage da ake tace man. Wakiliyar BBC Mayeni Jones da kuma Josephine Casserly sun yi bincike kan masana'antar.

Short presentational grey line

Bayan shafe awanni a mota da babur da kuma tafiya a ƙafa, mun isa wata haramtacciyar matatar man fetur - wani wuri da jami'an tsaro suka kai samame tare da rufe shi.

Tun kafin mutum ya ga komai zai fara jin warin man fetur. Sai kuma muka zo ƙarshen korayen bishiyoyin da suka lulluɓe wurin, sai kuma ga mu a wurin da wuta ta share.

Ana ganin alamun man fetur a dandariyar ƙasar wurin tare da ƙonannun saiwoyin bishiya. Ƙasar ta jigata har ma tana kama da inda aka samu aman wutar dutse.

Polluted creek

Asalin hoton, Fyneface Dumnamene/BBC

Bayanan hoto, Haramtattun matatun man fetur na ɓoye ne a ƙungurmin dazukan yankin Neja Delta

Wannan wani saƙo ne a Neja Delta da ya ƙunshi mahaɗar hanyar ruwa da ke kudancin Najeriya.

Ƙyallin mai duk ya mamaye saman ruwan da kuma wurin da alama bishiyoyi ne duk mai ya shanye itatuwansu.

Muna tare da wani ɗan siyasar yankin mai suna Chidi Lloyd da tawagarsa, inda ya yi mana bayani kan yadda aka kawo fetur ɗin da aka sato nan a jirgin ruwa.

Burnt-out oil refinery equipment

Asalin hoton, Fyneface Dumnamene/BBC

Bayanan hoto, Gungun miyagun da ke tafiyar da harkar tace haramtaccen fetur na da sarƙaƙiya sosai

Ana kunna wuta a ƙarƙashin wannan diro ɗin sannan a tafasa ɗanyen man fetur kuma a ware makamashi daban-daban daga ciki, daga fetur zuwa kalanzir da disel. Daga nan kuma sai a zuba fetur ɗin cikin wani mazubi da zai hutar da shi.

Sai dai ba ko yaushe ake samun nasarar yin hakan ba - kuma idan aka samu matsala, yana haifar da fashewa wadda za ta iya zama mai haɗari kamar wadda ta faru a Juma'ar da ta gabata.

Yawan mutanen da suka mutu ya nuna yadda sana'ar tace haramtaccen mai take samar wa dubban matasa aiki a Neja Delta tsawon shekaru da suka wuce - a ƙasar da rashin aikin yi ke ƙaruwa.

Ma'aikata kan shafe makwanni a matatun kamar wannan a lokaci guda, akasari kan yi aiki har cikin dare musamman ga waɗanda kyakkyawan tsarin aiki da ke da ƙwarewar harkokin kuɗi da ta iya aiki.

Gwamnati ta yi ƙiyasin cewa an sace mai da ya kai darajar dala biliyan uku. Ana sayar da wannan man ne ta ɓarauniyar-hanya a Najeriya ko kuma a kai shi ƙasar waje bayan sun sato shi ta hanyar fasa bututan mai na gwamnati.

Hadarin 'yunwa'

Gurɓacewar iskar da waɗannan matatun ke haifawa ba wai a garuruwan da ke kusa kawai ake jin ta ba.

Iskar gas ɗin da ake samu wajen samar da fetur na ƙonewa mafi yawan lokaci ta yadda ba za a iya sake amfani da shi ba ta hanyar abin da ake kira gas flaring wato ƙona gas. Sai dai ba haramtattun matatu ne kaɗai ke yin hakan ba - duk da sun saɓa wa doka - kamfanonin mai na yin hakan.

Polluted waterway
Bayanan hoto, Ruwan da ke yankin ya lalace sakamakon haɗuwa da man fetur

Sai dai a daidai lokacin da haramtacciyar sana'ar tace mai ke haɓaka, ƙona gas ma ya ƙaru kuma hakan ya ƙara gurɓacewar iska.

A bayyane ake jin hakan yayin da mutum ke shiga Fatakwal, wani babban birni a Neja Delta.

Wani murtukeken hayaƙi ya turnuƙe sama, wani zubin abin na ta'azzara ta yadda ba za ka iya ganin gabanka ba fiye da tsawon mita 30 (tsawon ƙafa 100).

Duk da an rufe tagogi, amma idan mutum ya kwana a garin sai ya fahimci hakan a hancinsa. Wani likita a asibitin yankin ya ce yana samun ƙaruwar marasa lafiya da ke da alaƙa da nimfashi, waɗanda ake alƙanatawa da gurɓacewar iskar.

Sai dai mutane irin su Osaja da ke zaune a manyan gidajen da ke cikin birni, wanda ya nemi kada mu bayyana sunansa na gaskiya, ya ce wannan sakamakon ba abin ƙi ba ne.

Ya faɗa mana cewa ya mallaki haramtattun matatun mai biyu kuma yana cikin masu safarar haramtaccen man da kuma tacewa da sayar da shi.

Tarin motocin tsere da yake da su da kuma kogin ninƙaya da ke gidansa sun tabbatar da dukiyar da yake da ita.

"Shin ya da cewa ka zauna cikin kyakkyawan muhalli amma kuma ka mutu da yunwa? Idan kana jin yunwa za ma ka ji ka shaƙi wani abu?

"Idan dalilin da ke jawo gurɓatar iskar yana kuma sama wa mutane sai ma ka manta da wani gurɓacewar muhalli," in ji shi.

Ganima

Wasu da suka kasa samun aikin yi sun yarda da hakan.

Wani mai sana'ar ɗukar hoto ya faɗa mana yadda ya fara aiki a wata haramtacciyar matata a cikin daji lokacin da ya gaza samun aikin yi.

Yana "dafa" ɗanyen man - wanda ke haifar da hayaƙi mai yawa da ma'aikata ke shaƙa. Ya ce idan aka samu matsala sukan gudu zuwa cikin gulbi (ko mahaɗar hanyar ruwa), amma ba ko da yaushe hakan ke zama mafita ba saboda idan akwai mai shi ruwan kan kama da wuta.

Haɗurran da ke cikin hakan suka sa ya haƙura da aikin.

Burned ground at an oil refinery

Asalin hoton, Fyneface Dumnamene/BBC

Bayanan hoto, Haramtattun matatun sun lalata ƙasa da kuma hanyoyi n ruwa da ke kusa da wurin

Amma wata da ta karanta ilimin kwamfuta kuma ta shiga harkokin tace fetur ɗin ta ɓarauniyar hanya bayan ta kasa samun aikin yi, ba ta damu da batun gurɓacewar muhallin ba.

Matar da ke da shekara 40 da ɗoriya na amfani da jirgin ruwanta wajen safarar mai daga matatun: "Ni mutuniyar ruwa ce, abin ba wahala a wajenmu."

Waɗanda ke sana'ar sun faɗa mana cewa idan har gwamnati za ta yi maganin tace haramtaccen fetur - kamar yadda Gwamnan Rivers Nyesom yake yi - to ya kamata a yi wani abu a kan rashin ayyukan yi.

Kazalika, suna ganin haramta harkar ba abu ne mai sauƙi ba ganin irin yawan mutanen da ke cikinta, ciki har da jami'an tsaro.

Osaja ya ce yana yawan biyan cin-hanci don kada a kai samame kan matatun nasa: "Kowa na cikin harkar nan. Tsararren laifi ne."

A gefe guda kuma, 'yan sanda na binciken zargin da gwamnan Rivers ya yi cewa wani babban jami'in ɗan sanda na gudanar da haramtacciyar matata.

Burnt-out vehicles

Asalin hoton, Arise TV

Bayanan hoto, Ƙonannun motoci ne kawai suka rage bayan wutar da ta tashi a haramciyyar matatar mai da ke Jihar Imo

Osaja na ganin harkar tace haramtaccen mai ba don samun kuɗi ake yi ba. Yana ganin kan sa a matsayin mai samun ganima daga kamfanonin mai kuma yana ba mutane.

Ƙauyensu wata cibiya ce da kamfanonin mai ke haƙo mai sosai amma har yanzu mutanen ƙauyen ba su da komai, inda suke da ƙarancin kayan more rayuwa, a cewarsa.

"Mun gamu da rashin adalci iri-iri. Me ake ba wa mazauna ƙauyuka? Babu komai! Ziro!

"Wannan kayanmu ne. Wannan kayana ne kuke kwashewa, me kuke ba ni? Saboda haka yanzu kowa ya ji ɗanɗanon haramtacciyar zuma da kuma daɗin da take da shi."

Map
1px transparent line