Abu biyar da ya kamata ku sani kan bututan man da ake shimfidawa daga Ajaokuta zuwa Kano

- Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
Yayin da albarkatun makamashi ke sake zama abubuwan da ke nuna alkiblar duniya, kasashe irin su Najeriya da ke da albarkatun na kara samun tagomashi a kasuwar duniya.
Ga kuma rikicin da ake yi na Rasha da Ukraine, wanda ya kara sanya bukatar makamashi irin su gas ta karu a yammacin duniya.
Ko a makon da ya gabata, sai da wakilan Tarayyar Turai suka je Najeriya domin neman ta kara yawan makamashin gas da take fitarwa zuwa kasuwar duniya.
Amma a iya cewa an yanka a kan gaba, domin kuwa gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayar da aikin shimfida bututan gas daga Ajaokuta na Jihar Kogi a tsakiyar ƙasar zuwa Kaduna, ya kuma tike a Kano.
Da yawan mutane ba su san wane irin alfanu ne a cikin wannan aiki ba ga Najeriya har sai an gama sun gani a kasa, in ji Malam Mele Kolo Kyari, wanda ya kai ziyara tashar farko da ake gudanar da ake aikin da ke Ajeokuta zuwa Sarkin fawa.
BBC ta kasance cikin wannan tawagar kuma ta tattaro abu biyar da suka kamata mutane su sani kan wannan aiki.
Za a shimfida bututan mai tsawon kilomita 614

Aikin wanda zai taso daga Ajaokuta na Jihar Kogi ya shiga Kaduna ya tike a Kano, za a jera bututai masu tsawon kilomita 614 a ƙasa.
Amma shugaban da ke jagorantar wannan aiki, Injiniya Ahmed Barwa, ya ce za a iya wuce tsawon adadin da aka yi hasashe, saboda wani wurin ya yi kasa sai an kara abin da aka yi kiyasi a baya.
"Za a dinga tura gas da ya kai biliyan 2000 a ma'aunin sqb ta wannan bututan," kamar yadda shugaban kamfanin mai na NNPC ya ce.
"Idan an samu nasarar kammala wannan aiki za a samu gas a duka yankunan kasar nan daga arewaci zuwa kudanci ko ina gas zai wadata".
"Za mu fara sa gas a wannnan bututan daga wata hudu na shekara mai zuwa ta 2023," in ji Mele Kyari.
Za a kara samun wutar lantarki

Asalin hoton, WS
Makamashin gas na daga cikin abubuwan da ake samun wutar lantarki da su a wannan zamani. Kasashen da suke da shi da yawa a mafi yawan lokuta ba su fiya rashin wutar lantarki ba.
Da wannan makamashi kasashe da dama na iya sarrafa yadda suke son su yi amfani da shi.
Cikin alfanun da za a samu a wannan aiki, gas din da za a rika aikewa ta cikin wannan bututan za su taimaka wajen samun karin wutar lanbatarki kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yi hasashe.
Abu ne a zahiri cewa karancin wutar lantarki na daga cikin abubuwan da Najeriya ke kokawa a kai a yau, musamman a wasu jihohi irin su Borno da rikici ya janyo aka rika lalata wutar.
Habbaka sabbin masana'antu
Kai-tsaye wannan na da alaka da maganar lantarki, wadda ke cikin abubuwan da ke korar masana'antu daga kasashe masu tasowa.
Duk wani mai kamfani ko masana'antar da zai rika fama da sayen man fetur ko gas domin tafiyar da ayyukansa zai koka kan cewa kusan kai da kai suke yi da ribar.
Idan wuta ta samu, akwai yiwuwar da yawan masana'antun da suka mutu a baya da wadanda suka bar Najeriya saboda kashe kudin da suke yi wajen tafiyar da wutar da za a samu duk za su dawo.
A gefe daya kuma, ana sa ran hakan zai janyo sabbin masana'antu su bude musamman a Jihar Kano da take da fuskar kasuwanci.
Samar da ayyukan yi

Daya daga cikin manyan matsalolin da ake fama da su a Najeriya shi ne rashin aikin yi.
Hatta matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar, ana alakanta ta da matsalar rashin aikin yi. Saboda mafi yawan wadanda suke da hannu cikin rikicin matasa ne da ya kamata a ce suna bakin aikinsu.
Gwamnati na ganin cewa idan wannan aikin ya tafi yadda aka tsara, matasa da dama a kasar za su samu abin yi da za su dogara da kansu. Watakila kuma hakan ya rage yawan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Samar da karin kudaden shiga
Ga gwamnati a dukkan matakai, wannan wani alfanu ne da za a jima ana amfana.
Da zarar masana'antu sun karu kudaden da ake karba na haraji za su karu a kasa da kuma jihohi, baya ga nauyi da za a dauke wa gwamnatoci na cewa sai ta ba wa kowa aikin yi.
Daidaikun mutane da masana'antu za su dinga biyan kudaden haraji da za a rika amfani da su wajen yin ayyukan raya kasa da tafiyar da wasu ayyukan gwamnati na yau da gobe.
Duka abubuwan da aka lissafa a sama na da alaka da wannan, domin idan babu lantarki ba za a iya samar da sabbin masana'antu ba. Kazalika, in babu sabbin masana'antu ayyukan yi ba za su samu ba.
Bugu da ƙari, duk wanda ba ya samu babu yadda za a yi ya biya haraji, kai ko hayar gidan da yake zaune ba zai iya biya ba.











