'Najeriya za ta fuskanci giɓin kuɗaɗe a fannin haƙo ɗanyen mai'

Yakin da Rasha ta kaddamr a Ukraine ya sanya farahin mai ya tashi a kasuwannin duniya

Asalin hoton, Getty Images

Ƙwararru sun fara tsokaci a kan asarar da Najeriya za ta iya yi, saboda kamfanin haƙo man fetur na Eni ya ayyana cewa ba zai iya cika alƙawarin man da ya ke fitarwa zuwa ƙetare ba.

Lamarin ya faru ne sakamakon fasa bututun mai a tashar haƙar man fetur ta Brass a yankin Nembe cikin jihar Bayelsa.

Kamfanin ya ce al'amarin zai haddasa giɓin sama da gangan dubu ashirin da ya ke samarwa a kullum.

Eni ya ce ba zai iya cimma yarjejeniyar samarwa wadanda za su sayi mai daga gare shi ba, sakamakon fashewar da bututan da ke daukar mai daga rijiyoyi zuwa wasu tashoshi a jihar Bayelsa.

Bugu-da-kari kamfanin na Eni ya ce ko a karshen watan jiya ma, sai da bututan mai a tashar Obama suka fashe al'amarin da ya janyo katsewar ganga dubu biyar daga man da ake hakowa.

Ko me hakan yake nufi Eni ya ce ba zai iya cika alkawarin fitar da mai ba?, Dr. Ahmad Adamu masanin tattalin arzikin man fetur a Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewa daman man fetur din da kamfanin Eni ke fitar bai taka kara ya karya ba.

Ya ce idan aka kwatanta da yadda ake fitar da shi a shekarun da suka gabata da kasar ke fitar da ganga miliyan biyi da rabi, daga baya aka koma fitar da ganga sama da miliyan daya, a yanzu kuma baki daya ganga miliyan 1.400,000 kacal Najeriyar ke fitarwa.

Sai dai Dr Ahmad ya ce a yanzu da farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya, dama ce da ya kamata Najeriya ta yi amfani da ita wajen kara adadin man da ta ke fitarwa, maimakon a ce an samu raguwa.

Ya kuma ce wannan ita ce asarar da ƙasar za ta tafka na rashin samun ƙarin kudi a fannin man fetur.

Baya ga wannan kamfanin mai na Eni ya kuma sanar da dakatar da aikin fitar da man a tashar Brass da kamfanin iskar gas na Bonny da kuma na Okpai.

Kamfanin bai yi cikakken bayani kan fashewar ba, to amma barnata wuraren ayyukan mai da bututan mai da sace su sun zama ruwan dare a Najeriya.

Abin tambayar shi ne ko wane tasiri matakin na Kamfanin Eni zai ga kasar? Ga abin da Dr Ahmad ke cewa:

''Duk lokacin da aka ara samun irin wannan matsalar a kasa, ya na ragewa danyan man kasar farin jini, wajen daidai farashinsa a matakin kasa da kasa zai sanya a dinga tsadar shi hakan zai shafi farashin saida shi kasancewar kowacce kasa ta na da farashin da ta ke saida man ta.

Sannan yanayin muhalli da siyasa da zamantakewa na taka rawa wajen yi wa danyan mai daraja a kasuwar duniya a duk loikacin da aka bukata.''

Kawo yanzu dai, dukkan bututan da ke kai mai daga rijiyoyi zuwa tashar Brass an katse su nan take don dakile tsiyayar mai da kuma gudun tashin wuta a wuraren da ake aikin hakar man.

Haka kuma, kamafanin na Eni ya ce ya jingine aikin samar da iska gas har kimanin cubic metres miliyan goma sha uku a kowacce rana.

Rahotanni sun ambato darakta janar na hukumar da ke sa ido kan malalar mai na Najeriya, Idris Musa na cewa dukkan haɗuran biyu ɓarnace da miyagu ke yi, sai dai babu cikakken bayani kan lamarin.