Zaɓen Faransa: Nasara mai cike da tarihi duk da Macron ya gurɓata siyasar Faransa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Hugh Schofield
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Paris
Kafin a ba da sanarwar samun nasararsa, yana da kyau a amince da girman nasarar da shugaba Macron ya samu.
Ko da yake wannan dai bai isa ba, amma shi ne karo na farko da aka sake zabar shugaban kasa a Faransa a jamhuriya ta biyar.
Gaskiya ne, shugabanni sun maimaita shugabancin Elysée a baya, amma duka biyun François Mitterrand a 1988 da Jacques Chirac a 2002 sun kasance sun tsinci dami a kala ne a tsakiyar masu adawa a lokacin da ake gudanar da zaɓe.
Dangane da nasarar de Charles de Gaulle ya samu a shekarar 1965, tun da farko jama'a ba za su yi shi ba.
Don haka Emmanuel Macron shi ne shugaban kasa na farko a wannan zamani wanda bayan tafiyar da kowane bangare na manufofin kasashen waje da na cikin gida na tsawon wa'adi, ya sake samun amincewar jama'a.
Sakamakon ya nuna cewa akwai miliyoyin Faransawa da ke jin cewa Emmanuel Macron ya yi kokari duk da wasu manya da ke ganin bai taka rawar a zo a gani ba, da kuma masu sukarsa a shafukan sada zumunta.
Wadannan mutane sun fahimci cewa rashin aikin yi ba batun siyasa ba ne, musamman saboda sauye-sauyen da Macron ya bijiro da su. Suna tsammanin yadda ya jagoanci yaki da korona ya nuna cewa cancanta, kuma sun yarda cewa babu abun da ya kamata su yi face yaki da masu son yi masa ritaya irin ta siyasa.

Asalin hoton, Getty Images
Sun kuma gane cewa suna da shugaba wanda zai iya kare su a fagen siyasar kasashen duniya. Suna farin cikin cewa mutumin da ke mulki a fadar Elysée zai iya yin gaba da gaba da Putin, koda kuwa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Kuma sun yi la'akari da cewa a karkashin Macron Faransa za ta iya jagorancin Turai, a daidai lokacin da hangen nesansa na samar da 'yancin cin gashin kai na soja da tattalin arziki ga EU ya fi dacewa.
Bambance-bambancen da ke akwai tsakaninsa da Marine Le Pen a bayyane suke ƙarara.
Wataƙila ba lallai ne wasu su so Emmanuel Macron ba, amma wadanda yake bukata sun fito sun kuma yi masa rana.
To sai dai bangare na biyu na tsarin Macron ya fi matsala, kuma a nan ne fa'idodin da ya samu suke.
Shekaru biyar da suka gabata, Macron ya yi wani abu da ka iya cewa ca-ca ne a yanayin siyasar zamani.
Ta hanyar karkata daga tsarin da aka saba tafiya a kai, ya lalata tsohuwar haɗin gwiwar masu ra'ayin mazan jiya da dimokiraɗiyya da kuma yin amfani da ikon da ke cikin Jamhuriya ta biyar ta De Gaulle, ya shigar da tsarin gwamnati na musamman zuwa fadar Elysée.
Manufofinsa sun riƙa sa 'yan adawa na kwafsawa har suka kai wani mataki da ya yi imanin ba za su iya haifar da barazana ba. Ya zuwa yanzu hakan ta tabbata kamar yadda sakamakon wannan zaben ya nuna.

Asalin hoton, Getty Images
Amma zaben ya kuma nuna wani abu dabam: cewa mutane da yawa a Faransa a yanzu suna shirye su yi tarayya da "masu tsaurin ra'ayi". Suna yin hakan ne saboda nasarar Macron ta nuna cewa babu inda za su je idan suna son adawa da shi.
Yawancin wadannan masu kada kuri'a musamman ma miliyoyin da suka zabi dan takarar jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi Jean-Luc Mélenchon, a yanzu suna son daukar fansa kan sabon shugaban kasar da aka sake zaba.
Suna fatan za su iya yin hakan a zaben 'yan majalisar dokoki da za a yi a watan Yuni. Amma idan wannan bai yi aiki ba, suna mafarkin wani "zagaye na uku" a watan Satumba, baya ga shirya zanga-zangar adawa da Macron a kan titi, musamman ma idan ya kaddamar da sabbin sauye sauye.
Emmanuel Macron ko shakka babu zai fara wannan wa'adi na biyu yana mai bijiro da sabon tsarin gudanar da gwamnati, zai fi sauraron jama'a a yanzu. Ya san akwai gyare-gyare.
Abin da ya fi damun shi shine yadda ya yi irin wannan alkawarin a baya, kuma mutane da yawa ba sa gaskata shi.
"Ba wai kawai wannan zaben ya nuna cewa akwai Faransawa guda biyu masu adawa da juna bane, ya kuma nuna yadda mutane ke kara kushe bangarorin da suke adawa da su," in ji wata mai sharhi Natacha Polony.
"A zabukan da suka gabata ana kammala su da samun mutum guda da ake kallo a matsayin shugaban kowa da kowa a Faransa, bana jin haka abun yake a yanzu''.














