Ɗaliban Chibok: Me ya sa Hassana ba ta samu gatan da sauran ɗaliban da aka sako suka samu ba?

Hassana Adamu

Asalin hoton, Rebecca Galang

    • Marubuci, Adaobi Tricia Nwaubani
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Abuja

Cikin jerin wasiƙun da 'yan jarida daga nahiyar Afirka ke aiko mana, 'yar jaridar Najeriya Adaobi Tricia ta tattauna da wata ɗaliba da aka ceto daga hannun Boko Haram wadda kuma ta fuskanci yanayi na musamman saɓanin 'yan uwanta da aka ceto tun farko yayin da ake bikin cika shekara takwas da faruwar lamarin.

Short presentational grey line

Hassana Adamu na cikin farin cikin komawa gida bayan shekara kusan takwas da sace ta da 'yan bindigar Boko Haram suka yi daga makarantarsu a garin Chibok na arewa maso gabashin Najeriya. Sai dai ta damu saboda ba ta samu tarɓa ta musamman da sauran 'yan uwanta suka samu ba da aka ceto kafin ta.

"Ina so gwamnati ta taimaka min da abubuwa masu amfani," kamar yadda ta faɗa min. "Ina so na koma makaranta don na yi rayuwa managarciya."

Hassana mai shekara 18 a lokacin, tana cikin 'yan mata fiye da 200 da aka sace daga makarantar sakandarensu a daren ranar 14 ga watan Afrilu na 2014. Ita da ƙawayenta biyu sun koma gida a watan Janairu, abin da ya sa adadin waɗanda aka sako zuwa fiye da 100.

Tsakanin 2016 da 2018, sojojin Najeriya sun ƙwato ko kuma an sako ɗalibai uku a Dajin Sambisa, yayin da aka sako 103 sakamakon tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da 'yan Boko Haram.

Dawowarsu ta haddasa murna da bukukuwa a faɗin duniya. Kafofin yaɗa labarai na ƙasashen duniya suka dinga yaɗa labarinsu da hotunansu. Shi ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyace su zuwa fadarsa, Abuja inda gwamnoni da sauran ƙusoshin gwamnati suka halarta.

Rescued Chibok girls wearing blue Hijabs

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An yi ta biki bayan kuɓutar da rukunin farko na 'yan matan Chibock

An sauke su a masaukin gwamnati tsawon watanni a Abuja, inda aka ba su horon wanke tunani da gwamnati ta ɗauki nauyi. Aka dinga ciyar da su kyauta da ba su tufafi kyauta. Mutane da dama daga ƙasashen duniya sun kawo musu ziyara, ciki har da wadda ta lashe kyautar Nobel 'yar Pakistan Malala Yousufzai.

Daga nan kuma, aka tura su yin kwas na musamman a Jami'ar Amurka da ke Yola wato American University of Nigeria (AUN), wanda gwamnatin Najeriya ta ɗauki nauyi. Shekara huɗu bayan haka, har yanzu gwamnati na ɗaukar nauyin waɗanda suka yarda su ci gaba da karatu daga ɗaliban na Chibock a AUN.

'Ko don saboda ina da aure ne?'

"'Yan matan da ke makarantar ne suka faɗ min yadda gwamnati ke kula da su," a cewar Hassana wadda ta yi magana da ƙawayen nata ta waya tun bayan komawarta gida. "Sun faɗa min yadda suka zauna a Abuja kafin su koma makaranta."

"Saboda mun daɗe ne ko kuma saboda da ma muna da aure ne? Babu mamaki dalilin da ya sa kenan gwamnati ba ta so ta kula da mu," in ji ta.

Hassana ta auri ɗan Boko Haram shekara biyu bayan kama ta - kuma mijin nata na cikin waɗanda suka miƙa wuya ga sojojin Najeriya a shekarar da ta gabata sakamakon matsin lamba da suke fuskanta daga dakarun Najeriya. Rundunar sojan ta ce masu iƙirarin jihadi 7,000 ne suka miƙa wuya a wani mako ɗaya na watan Maris.

Hassana da mijinta sun zauna a Maiduguri tsawon kusan wata biyar a wasu sansanonin tubabbun 'yan Boko Haram da matansu. Bayan haka, an tura ta gida da 'ya'yanta biyu zuwa gida, shi kuma mutumin ya koma wajen 'yan uwansa a garin Banki da ke kan iyaka.

"Ba auren gaskiya ba ne," in ji ta. "Ina buƙatar rayuwa mai kyau ni da yarana. Ba zan taɓa komawa wajensa ba."

Wasu 'yan Chibok biyu, Ruth Ngaladar da Halima Ali Maiyanga, su ma sun rabu da mazajen nasu.

"An sake su ɗauke da yara kuma aka tura su gida ba tare da komai ba," a cewar Yakubu Nkeki, shugaban ƙungiyar iyayen da aka sace 'ya'yansu. "Waɗannan yaran uku suna fama sosai."

Mista Nkeki ya nuna damuwa cewa rashin mayar da hankali kan 'yan matan na Chibok da gwamnati ke nunawa na nufin sauran 109 da har yanzu ke hannun 'yan bindigar ba lallai ne su sake haɗuwa da iyayensu ba, ko da kuwa za a iya ceto su.

line

Ministar Harkokin Mata Dame Pauline Tallen ta faɗa min cewa har yanzu Buhari bai samu damar ganawa da 'yan matan uku ba har yanzu, amma zai yi hakan ba tare da damuwa ba idan dama ta samu.

"'Yan mata kusan biyar ne ke kiran iyayensu daga Dajin Sambisa. Suna cewa sun kan dutsen Gwoza," a cewar Mista Nkeki.

"Kusan biyar suna tare da gwamnatin jihar. Yaran na kiranmu. Ɗaya daga cikinsu ta kira iyayenta lokacin da muke ganawa kuma ya saka muryarta a fili don mu ji abin da take faɗa. Ba mu sani ba ko gwamnati ta san cewa yaran Chibock ne."

Ƙaruwar satar yara a makarantu

Ko da a ce gwamnati ta san daga inda suke ba lallai hakan ya yi wani tasiri ba. Ɗaliban Chibok sun tsinci kansu cikin wani abin mamaki - yaran da aka sace daga ɗakin kwanansu na makaranta. Amma cikin shekara biyu da suka wuce, Najeriya ta fuskamnci ƙaruwa a sace-sacen yara a makarantu da 'yan fashin daji ke yi.

Ɗalibai aƙalla 1,409 aka sace daga makarantunsu a Najeriya cikin wata 19 na tsakanin Maris 2020 da Satumban 2021, a cewar wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SBM, kuma an biya aƙalla miliyan 220 a matsayin kuɗin fansa.

Yayin da ake cewa gwamnati Najeriya ta biya Boko Haram yuro miliyan uku don karɓo 'yan matan Chibok, gwamnatin ba ta fiya shiga waɗannan sace-sacen na baya-bayan nan ba. Iyaye da 'yan uwa ake bari da biyan kuɗin fansa don karɓo yaransu.

Duk da haka, Hassana Adamu ta yi imanin cewa tana da haƙƙi kamar sauran ƙawayen karatunta. Ko ba komai, tana so a saka ta cikin tallafin karatu na jami'ar AUN.

"Abin na damu na sosai saboda tare muka fara shan wahalar nan amma sauran 'yan matan sun zama kamar Amurkawa ni kuma ina nan a gida ina kula da yara," a cewarta.

Map of Nigeria showing Borno state, Chibok, Sambisa Forest, Maiduguri, Abuja and Lagos
line