Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Sojojin Rasha sun yi min fyade kuma suka kashe mijina'
Sojojin Rasha sun janye daga yankunan da ke kusa da Kyiv, to amma sun bar rayuwar wasu da tabon da ba zai taba warkewa ba, inda suka yi wa mata fyade tare da kashe mazajen wasu, kamar yadda wasu da abin ya shafa suka bayyana wa BBC.
A wani yanki da ke da nisan kilomita 70 a yammacin Kyiv BBC ta tattauna da wata mata mai shekara 50 wadda aka sauya mata suna zuwa Anna domin tabbatar da sirrinta.
Matar ta sheda wa BBC yadda wani sojan Rasha ya shigo gidansu a ranar 7 ga watan Maris inda ya rutsa ta da bindiga ya fita da ita zuwa wani wuri da barzanar zai hallaka ta idan ba ta ba shi hadin kai ba.
Ta bayyana yadda sojan ya yi mata fyade. Kuma ta ce bayan ta dawo gida ta ga an harbi mijinta a ciki ya rasu.
Kasashen tsakiyar Turai za su gana kan rikicin na Ukraine
Ministocin harkokin waje na kasashe biyar na tsakiyar Turai na shirin ganawa a wani wuri kusa da Prague, babban birnin Jamhuriyar Czech, ranar Talata domin tattauna batun yakin Ukraine, lamarin da shi ne na gaba-gaba a jerin abubuwn da za su gana a kai.
Ana ganin yakin ya fito da barakar da ke tsakani a kasashen tsakiyar Turai a kan yadda za a tunkari barazanar Rasha ta mamaye, wanda wannan abu ne da ya haddasa kalubale ga tsarin diflomasiyyar yankin.
Akwai akalla bangarori daban-daban guda biyar a yankin tsakiyar Turai, masu ra'ayoyi da fahimta daban-daban, inda a wani lokacin suke kasance kusan daya a wani lokacin kuma suke sabani da juna.
Wannan da ake kira ''Central 5'' da ya kunshi kasashen Austria da Jamhuriyar Czech da Slovakia da Slovenia da kuma Hungary, idan ana magana ne kan Ukraine, to suna da bambanci sosai a tsakaninsu.
Kasashen Czech da Slovakia sun yarda a aika wa Ukraine motocin yaki na igwa da kayan kariya ta sama. Su kuwa 'yan Hungary sun kasance ne 'yan ba-ruwanmu.
Wata kungiyar kuma wadda kusan ta fi dadewa a tsakiyar Turan mai suna ''Visegrad Four'' kusan a ce ta kusa tarwatsewa a kan halin ko-in-kula da gwmnatin Hunagry ta game da yakin na Ukraine.
Abu ne mai wuyar gaske a ga yadda kasashen wannan kungiya za su kasance tsintsiya madaurinki daya.
Zargin Fyade
Yayin da ake ci gaba da yakin hukumomin UKraine sun ce suna gudanar da binciken zargin da wasu mata suka yi na cewa sojojin Rasha sun yi musu fyade.
Sun ce suna tattara yawa da kuma shedun laifin da ake zargin aikatawa, wadanda suna daga cikin daruruwan da ake zargi sojin na Rasha sun aikata a kan farar hula.
Wani wakilin BBC ya saurari bayani daga wasu matan da ssuke zargin an yi musu wannan cin zarafi, kuma ya samu shedar da ke nuna sojojin mamaye na Rasha sun yi wa matan Ukraine fyade.
Sai dai fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta musanta cewa sojojinta sun aikata laifukan.
Ukraine na kir ga majalisar Dinkin Duniya da ta kafa wata kotu ta musamman da za ta hukunta Shugaban Rasha Vladamir Putin da kansa a kan zargin laifukan yaki ciki har da fyade.
Wata kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Ukraine mai suna, La Strada-Ukraine, ta zargi dakarun Rasha da amfani da fyade a matsayin makamin yaki.
Shugabar kungiyar, Kateryna Cherepakha, ta yi magana da Majalisar Dinkin Duniya:
Ta ce, '' Mun ga tsananin dimauta, tsoron rayuwa, tsoron a yi magana a kan abin da ya auku. Wadanda suka yi sa'a suka tsira" zuwa wani wuri tudun-mun-tsira suna cikin kaduwa sosai da ba za su iya fadar abin da ya faru ba.
Suna bukatar tallafi, da kulawar yadda za su dawo hayyacinsu, da farko.
Mun san cewa da yawa daga cikin wadannan laifuka abu ne mai wuya ko ma a dai a ce kila ba za a taba bayyana su ba, saboda abin takaicin yawancin wadanda aka aikata wa sojojin mamaye na Rasha sun kashe su.''
Shugabar ta kara da cewa kungiyarta ta samu kiran waya na zargin sojin Rasha da aikata laifukan fyade.