Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ukraine za ta gamu da matsalar tattalin arziki - Bankin Duniya
Bankin Duniya ya ce yana sa ran tattalin arzikin Ukraine ya yi baya da kashi 45 cikin dari a shekaran nan sakamakon yakin da kasar ke yi da Rasha.
Haka kuma bankin ya yi hasashen samun gagarumin nakasu ga tattalin arziki fiye da wanda annobar korona ta haifar a fadin gabashin Turai da yankin tsakiyar Asia, inda takunkumin da ba a taba gani ba da ake sanya wa Rasha, shi ma zai haifar da koma-bayan tattalin arziki sosai ga Rashar ita ma.
Tuni daman fadan ya raba dubban mutane da rayuwarsu, kuma bai tsaya a nan ba domin tattalin arziki ma na kasashe ya shiga halin ha'ula'i a sanadiyyar yakin.
Mamayar ta Rasha, ta tilasta wa yawancin ma'aikatan Ukraine tserewa ko kuma barin wuraren aikin domin su je fagen daga su kare kasarsu.
An rufe harkokin kasuwanci, an lalata tituna da masana'antu da kuma sauran kayayyakin jin dadin jama'a a kasar. Kan hakan Bankin Duniya ya ce, yakin ya yamar da hannun agogo baya tsawon shekaru kan cigaban da aka samu a kasar, ba ma ita kadai ba har ma makwabtanta suma suna jin tasirin yakin.
Ukraine babbar kasa ce da ke samar da kayan abinci a duniya, kamar su man girki da alkama, to amma yanda wannan yaki ya dakatar da samar da kayayyakin, kasar ta yi asarar muhimmiyar hanya ta samun kudade da samar da ayyuka.
Bankin Duniyar ya ce yakin ba karamar illa ya yi kuma zai ci gaba da yi ba ga tattalin arzikin Ukraine, kuma ana bukatar gagarumin tallafi na kudi na nan da nan domin tabbatar da ci gaba da dorewar gwamnatin Shugaba Zelensky, tare kuma da tallafa wa al'ummar kasar su jure wa duk matsaloli da wahalhalun da ke tattare da yaki.
Tuni bankin ya bayar da taimakon kusan dala miliyan dubu daya kuma ya yi alkawarin bayar da wani tallafin na wata dala miliyan dubu biyu a watanin da ke tafe.
Tarin takunkumin da ake ta sanya wa Rasha, wanda ba ta taba ganin irinsa ba a baya, ya sa bankin na duniya ya yi hasashen cewa ita ma Rasha tattalin arzikinta zai ragu da sama da kashi 11 cikin dari a shekaran nan.
Makwabtan kasashe irin su Belarus da Kyrgyzstan da Moldova da Tajikistan suma za su iya gamuwa da koma-bayan tattalin arziki a sanadiyyar yakin.
Kasashe a fadin yankin tsakiyar Turai da tsakiyar Asia, suma mai yuwuwa su gamu da matsalar raguwar bunkasar tattalin arzikinsu saboda faman da suke yi da tarin 'yan gudun hijira da ke tururuwa zuwa cikinsu, da raguwar samun kudaden da suke yi daga Rasha tare kuma da tashin farashin kusan komai kama daga abinci zuwa mai.