Har yanzu ba a ji duriyar mutum168 ba na harin jirgin kasan Abuja-Kaduna - NRC

Jirgin kasan da aka kai wa hari a baya
Bayanan hoto, Bayanai sun tabbatar da cewa an sace mutane da dama sannan aka kashe wasu

Wani rahoton da hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa akwai fiye da mutum 168 da ba a ji ɗuriyarsu ba, cikin wadanda harin da aka kai kan jirgin kasan nan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ya ritsa da su.

Mako guda kenan da wasu ƴan bindiga suka kai harin ta hanyar ɗąna bom a kan hanyar jirgin.

Hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriyar ta bayyana cewa tana bin hanyoyi daban-daban wajen bibiya da ƙididdigar makomar fasinjoji ko matafiyan da harin ƴan bindigan ya ritsa da su.

Alkaluman da hukumar ta fitar na baya-bayan nan a cikin sanarwar da take fitarwa lokaci zuwa lokaci, wadanda shugaban hukumar Injiniya Okhiria yake sanya wa hannu, sun nuna cewa daga cikin fasinja 362, wadanda ta san cewa sun hau jirgin, zuwa yanzu dai ta tabbatar da cewa 186 sun isa gidajensu.

Sai dai lambar wayar mutum 51 na wasu daga cikin ragowar matafiyan kuma ba a kama su - wato wasu daga ciki ko dai a kashe suke, ko kuma ba a iya kama su, tun daga ranar Talatar da ta wuce zuwa yau.

Wayoyin mutu 35 da biyar kuma daga ciki kuma ana kama su, suna kuwwa, amma ba a amsa kiran.

Harwayau, akwai wasu layukan waya 60 na wasu matafiyan da ke jikin jerin sunayensu, wadanda idan aka buga sai na'urar ta ce layukan wayar ma ba su taɓa wanzuwa ba.

Kazalika a cewar hukumar sufurin jiragen kasan, kimanin matafiya 22 ba a ji ɗuriyarsu ba, wato sun ɓata.

Kuma iyalai ko danginsu ne suka sanar da hukumar cewa har yanzu ba su ga ƴan uwan nasu mutum 22 ba.

Idan ya tabbata lambobin wayar da ake magana na ɗaiɗaikun fasinjojin da suka sayi tikitin jirgin ne, to za a iya cewa har yanzu ba a san makomar fiye da mutum dari daga cikin matafiyan ba.

Sai kuma mutum takwas, wadanda hukumar ta ce sun riga mu gidan gaskiya, sakamakon harin.

A ranar Litinin din makon jiya da maraice ne ƴan bindiga suka kai hari kan jirgin kasan, inda aka yi ta samun bayanai masu cin karo da juna dangane da yawan matafiyan da ke cikin jirgin, har wasu na cewa kusan mutum dubu daya a cikin jirgin.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

Abin da ya faru tun da farko

Tun da fari, majiyoyi daga asibitin 44 na Jihar Kaduna da aka kai wasu daga cikin mutanen da harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun ce mutum bakwai ne suka mutu.

Kazalika sun ce mutum ashirin da biyu suka jikkata. Wakilin BBC da ya kai ziyara asibitin a lokacin, Yusuf Tijjani, ya ce ana kula da mutanen da suka jikkata a sashen bayar da kulawar gaggawa na asibitin.

Hukumar Kula da Safarar Jiragen Kasa ta Najeriya ta dakatar da jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna bayan kai harin kan jirgin kasan da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.

A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita da safiyar nan, ta ce "saboda wasu dalilai da ba mu shirya musu ba, mun dakatar da jigilar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna. Nan gaba za mu yi muku karin bayani idan akwai".

Wannan layi ne