Harin da aka kai wa jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna ya fusata 'yan Najeriya

Asalin hoton, Nig Army
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Harin da 'yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin da daddare ya ɗaga hankulan ƴan Najeriya tare da sanya fargaba a zuƙatan mutane da dama.
Al'amarin ya jawo asarar rayuka da har yanzu hukumomi ba su fadi yawansu ba, sannan wasu sun jikkata sakamakon buɗe wuta da maharan suka yi bayan da jirgin ya taka bam din da suka dasa a kan hanyarsa.
Wannan batu ya zama matsalar tsaro ta baya-bayan nan mafi muni da ta faru a ƙasar da kuma ta ɗimauta mutane, musamman ganin akwai a ƙalla fasinjoji 970 a cikin jirgin.
Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama jigo mai sada miliyoyin mutane da arewacin ƙasar daga babban birnin tarayya Abuja da kuma kudanci.
Hakan ne ya sa mutane suka fi raja'a da bin jirgin ƙasan ganin yadda ya zama wata hanyar sufuri da mutane suke ganin ita ce mafi tsaro, fiye da bin hanyar mota, yayin da jirgi kuma ya yi tsadar da sai masu ido da kwalli ne za su iya biya.
A shafin tuwita an yi ta musayar ra'ayoyi inda aka yi amfani da maudu'an #Nigeria da #Kaduna sau kusan 100,000, a Facebook kuma a kalla sama da mutum 68,000 ne suka tattauna kan batun.
Tuni dai gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya kai ziyara asibiti don duba majinyatan, sannan kuma mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ma ya je jaje Kadunan.

Asalin hoton, Kaduna Govt
Me mutane ke cewa?
Da dama ƴan Najeriyar da ke magana a kan batun sun fi nuna halin ruɗani da tashin hankalin da lamarin ya jefa su a cikin ne, musamman bayan yaɗuwar bidiyo daban-daban da ke nuna na cikin jirgin wasu jina-jina wasu kuma suna ta koke-koke.
Wasu kuma sun ta'allaƙa laifin harin ne a kan gwamnatin ƙasar, suna masu cewa ta daɗe da gazawa wajen shawo kan matsalar yaƙi da ƴan bindiga, musamman batun da ya shafi tare jirgin ƙasa wanda shi ne na biyu da maharan suka yi ƙoƙarin tare shi.
Duk da cewa dai na farkon ba su yi nasara ba kuma bai yi munin haka ba.
Ga dai abin da wasu ke cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
MrMacaroni @mrmacaronii ya ce: "Ina jajanta wa dukkan wadanda wani lamari mai muni ya taɓa rutsawa da su tun kafa Najeriya har zuwa yau.
Ina jin cewa ya kamata mu nemi Allah Ya shiga lamarinmu amma na sani sarai cewa Ubangiji ya albarkaci ƙasar nan da duk wani abu da take buƙata don yin nasara a matsayin ƙasa.
Ƴan Najeriya ne kawai za su iya ceto ƙasarsu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Shi kuwa wani mai suna A$AP Lerry @_AsiwajuLerry cewa ya yi: "Har yanzu addu'ar fita daga gida da koma wa lafiya ba ta da tabbas musamman a wannan yanayi da ake ciki a Najeriya. Allah dai Ya ci gaba da kula da mu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
valking @_VALKlNG ya ce: "Idan har akwai abin da za ka haƙura da shi a rayuwa to ban da haƙuri kan ƙoƙarin barin Najeriya."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Yayin da ita kuma Surayyah Ahmad ta ce: "Idan ka yanke shawarar barin Najeriya, ai sai dai idan za ka kwashi dukkan iyalanka da danginka kaf, in ba haka ba, abin zai ta bibiyarku ne.
"Zaɓi ɗaya muke da shi, mu haɗa kai dukkanmu don gyara ƙasar nan. Ba wallafa saƙonni a tuwita kawai za mu yi ta yi ba."
Wace waina ƴan Facebook kuma suka toya?

Asalin hoton, Kaduna Govt
Aliyu Dahiru Aliyu ya ce: "Wai ko dai Aisha Buhari ta hango abin da zai faru ne shi yasa kwana biyu da suka wuce ta wallafa saƙo cewa a yi wa Najeriya addu'a? Tabbas, kawai dai tana cike da fargabar cewa a ko yaushe kuma a ko ina wani mummunan abu ka iya faruwa a kowane ɓangare na ƙasar.
"A yanzu dai ba mu da tabbas kan gobenmu, kai ko da awa ɗaya mai zuwa ma babu tabbas a kanta."
Ibrahim Musa ya ce: "Lamarin Lanjeriya ya kai mizanin a hau buzu a rika jan Hasbunallahu ba adadi.
"Bandits (ƴan bindiga) sun zama abin da da suka zama. Yau su ɓalla da ƙarfi su shiga filin jirgi da tsakar rana, gobe su tare jirgin kasa a hanya. Dama ba a maganar masu hawa mota.
"Wani abun kamar a mummunan mafarkin amma kuma zahiri ne. A yadda aka dauko hanya a yanzu fa abin da akwai ban tsoro.
"Abin takaici shugabanninmu ko a jikinsu. Su dai su hau motoci su yi jerin gwano suna murmushi a cikin kayan alatu da giyar mulki. Lagwadar mulki ce kawai a gabansu ba hidimar al'umma ba. Komai ya sururuce.
"Allah Ya shiga lamarin kasarmu. Allah Ya kubutar da al'ummarmu. Hasbunallahu.."
Abdulaziz Tijjani kuwa cewa ya yi: "Sun fara kai hari tashar jirgin sama, kamfanunnunka sun dakatar da jigilar jirgin sama.
"Sun kai hari a kan jirgin kasa, an dakatar da jigila da jirgin kasa. Ga shi kuma sun dakatar da hanyar mota. Kuma fa akwai gwamnati a kasar!."


A shafin BBC Hausa kuma yaya ta kaya?

Kusan dukkan labaran da aka wallafa masu alaƙa da harin a shafukan sada zumunta na BBC Hausa sun samu tsoakaci daga mutane da dama, inda mafi yawansu addu'o;i suka yi na neman tsari sai kuma masu kushe hukumomi.
Amb Auwal Muhd Danlarabawa ya ce: "Wayyo Allahna! Wannan lamari sai ba daɗi, ana ta kashe mutane kamar dabbobi a kwata, haba wannan wacce rayuwa muke yi a kasar nan? Ko ina kisa. Kisa. Kisa. 😭😭😭".
Fatima Saminu ta ce: "Rayuwa kenan! Gwamnatin nan ta gaza babu abinda za a yi wa talaka a biya shi irin a ba shi tsaro, a inganta lafiyarsa, a samar da ilmin 'ya'yansu da samar da aikin yi.
"Ina miƙa sakon ta'aziyya ga waɗanda suka rasa rayukansu. Waɗanda suka samu raunuka kuma Allah ya ba su lafiya.
Kuma mu sani ƙuri'armu 'yancinmu, mu nuna ma gwamnatin nan mun san ciwon kanmu don Allah. Khairan Insha'Allah."
Me Shugaba Buhari ya ce?

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wa jirgin kasan, yana mai bayyana al'amarin a "matsayin wani abin damuwa matuka."
A cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar, Buhari ya ce, "kamar sauran 'yan Najeriya, ina cikin jimami matuƙa da faruwar wannan lamarin, wanda shi ne irinsa na biyu, wanda ya kai ga sanadin mutuwar fasinjojin da har yanzu ba a tantance adadinsu ba da kuma wasu da suka samu raunuka."
"Harin da aka kai kan jirgin kasa, abin takaici ne; tunani na yana kan iyalan waɗanda suka rasu da kuma addu'a ga wadanda suka jikkata," in ji Buhari.
Shugaban ya ce ya bayar da umarnin gaggawa na tabbatar da bincike da hanyoyin magance matsalar tsaron titin jigin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna.
Sannan ya umarci jami'an tsaro su kuɓutar da fasinjojin da da aka sace tare da farautar ƴan bindigar.

Babban hafsan sojin Najeriya ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasa hari

Asalin hoton, Nig Army
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya laftanal Janar Faruk Yahaya ya kai ziyara inda aka kai wa jirgin ƙasan hari.
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa hotunansa a Facebook tare da tawagarsa ta sojoji a wurin da aka kai harin.
Sanarwar ta ce ya tafi ne domin diba yanayin wurin da girman harin.
Ya kuma umarci sojoji da su tsawaita bincike domin kuɓutar da mutanen da aka sace.












