Gaskiyar bidiyon da aka yaɗa na harin ƴan bindiga a filin jirgin saman Kaduna

Asalin hoton, Others
An yi ta yaɗa wani bidiyo da aka naɗa a wani filin jirgi a Najeriya ana cewa na harin da ƴan bindiga suka kai filin jirgin saman Kaduna ne a ranar Asabar.
Mutanen da suka yi ta yaɗa bidiyon a manhajojin Whatsapp da Facebook da sauransu sun ce mutanen da ake iya gani a kan babura daga cikin wani jirgi da yake ƙoƙarin tashi ƴan bindigar ne da suka yi ƙoƙarin tsayar da jirgin da ƙarfi don kar ya tashi.
Sai dai ainihin bidiyon ba na harin da ƴan bindiga suka kai filin jirgin saman Kaduna ba ne.
Sashen binciken ƙwaf na BBC ya bi diddigin bidiyon inda ya gano cewa tun shekarar 2018 aka yaɗa shi a Tuwita.
Bidiyon tsoho ne tun na shekarar 2018 da aka ɗauka a lokacin da wasu magoya bayan wani ɗan siyasa suka kutsa kan titin tashin jirgi a filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sokoto.
Wani abu da ya kamata a lura shi ne idan da harin ƴan bindiga ne da mai ɗaukar bidiyon ba zai samu kwanciyar hankalin da zai ɗauka a yadda aka gan shi ba.
Sannan mutanen da suke kan baburan ba sa ɗauke da makamai, a zahiri ma ana ganin su suna ɗaga hannayensu ne alamar maraba.
Wata jaridar intanet ta wani fitaccen ɗan jarida Jafar Jafar ma ta wallafa bidiyon a shafinta na Facebook.
Amma daga baya mawallafin jaridar Jafar ya bayar da haƙurin kuskuren da aka yi bayan cire bidiyon.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya fitar da sanarwar ƙaryata batun bidiyon da cewa shi ne na harin da aka kai.
Babu karin bayanai
Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.Karshen labarin da aka sa a Facebook
A lokacin da lamarin ya faru an samu ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumuntar Najeriya bayan da bidiyon ya yaɗu kamar wutar daji, inda mutane suke surutu kan dalilin da zai sa mutane su yi irin wannan "gidadancin" don goyon bayan wani ɗan siyasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wani mai suna Diaryofapilot @_diaryofapilot a lokacin ya rubuta a Tuwita cewa: "A yanzu haka ga abin da ke faruwa a Sokoto... Magoya bayan wani ɗan takara da dama sun cika hanyar da jirgi ke bi... Ta ina muka kuskuro ne a matsayin ƙasa? 😥😥😥😅😅
Daga baya ne kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa ɗan siyasar da magya bayan nasa suka cika filin jirgin tsohon gwamnan Sokoto ne Aliyu Wammako.
agoya bayan sun fasa shingen filin jirgin suka kutsa don yi wa ubangidansu maraba a yayin da jirgin da yake ciki ke sauka don ya tsaya.
Harin da ƴan bindigar suk kai filin jirgin saman Kadunan ya yi sanadin mutuwar ma'aikata biyu na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman Najeriya (FAAN), kafin daga bisani jami'an tsaro su fatattake su, kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta ce.
Ƴan bindiga waɗanda a yanzu kotu ta ayyana su a matsayin ƴan ta'adda suna ci gaba da addabar jihar Kaduna da maƙwabtan jihohi a raewa maso yammacin Najeriya tsawon shekaru.
Yankin da ke kusa da filin jirgin saman Kaduna sun zama cibiyar hare-hare da satar mutane.
Ko sace ɗaliban Makarantar Karatun Ilimin Gandun Daji ma da kuma sace wani soja da aka taɓa yi a Makarantr Hirar da Sojoji ta NDA duk a kusa da wajen suka faru.











