Hotunan sabon kamfanin yin taki na Dangote da Buhari ya kaddamar

Kamfanin sarrafa taki na Dangote

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Kamfanin zai samar da ton miliyan uku na takin zamani duk shekara.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da babban kamfanin sarrafa takin zamani a jihar Legas, wanda attajirin Africa, Alhaji Aliko Ɗangote ya gina.

Kamfanin na yankin Ibeju Lekki a Lagos, wanda aka bayyana ya laƙume dala biliyan 2.5.

Kamfanin zai samar da ton miliyan uku na takin zamani duk shekara.

Kamfanin takin na Dangote zai taimakawa Najeriya rage dogaro da takin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.

Kamfanin Dangote ya kuma ce kamfaninsa na taki zai taimakawa ƙasashen Afirka dogaro da kansu wajen samar da abinci da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje.

Kaddamar da kamfanin na zuwa a daidai lokacin da farashin taki ya tashi sakamakon yaƙin Rasha a Ukraine, inda Rasha ce wadda ta fi samar da takin zamani a duniya.

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya kaddamar da kamfanin ne a Legas a ranar Talata
Kamfanin taki na Dangote, shi ne mafi girma a Afirka.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Kamfanin taki na Dangote, shi ne mafi girma a Afirka.
Kamfanin ya mallaki fadin fili hekta 500 a yankin masana'antu da ke Lekki, a Legas Najeriya

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Kamfanin ya mallaki fadin fili hekta 500 a yankin masana'antu da ke Lekki, a Legas Najeriya
Kamfanin Dangote ya ce yana haɗin guiwa ne da ƙungiyar manoma da kuma gwamnatocin jihohi na Najeriya da gwamnatoci na ƙasashen Afirka da ke son inganta aikin noma.

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Kamfanin Dangote ya ce yana haɗin guiwa ne da ƙungiyar manoma da kuma gwamnatocin jihohi na Najeriya da gwamnatoci na ƙasashen Afirka da ke son inganta aikin noma.
Taron kaddamar da kamfanin takin ya kunshi gwamnonin Najeriya

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Taron kaddamar da kamfanin takin ya kunshi gwamnonin Najeriya
Bikin kaddamar da kamfanin ya kunshi manyan 'yan siyasa a jam'iyyar APC

Asalin hoton, @SpeakerGbaja

Bayanan hoto, Bikin kaddamar da kamfanin ya kunshi manyan 'yan siyasa a jam'iyyar APC