Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan sabon kamfanin yin taki na Dangote da Buhari ya kaddamar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da babban kamfanin sarrafa takin zamani a jihar Legas, wanda attajirin Africa, Alhaji Aliko Ɗangote ya gina.
Kamfanin na yankin Ibeju Lekki a Lagos, wanda aka bayyana ya laƙume dala biliyan 2.5.
Kamfanin zai samar da ton miliyan uku na takin zamani duk shekara.
Kamfanin takin na Dangote zai taimakawa Najeriya rage dogaro da takin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Kamfanin Dangote ya kuma ce kamfaninsa na taki zai taimakawa ƙasashen Afirka dogaro da kansu wajen samar da abinci da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje.
Kaddamar da kamfanin na zuwa a daidai lokacin da farashin taki ya tashi sakamakon yaƙin Rasha a Ukraine, inda Rasha ce wadda ta fi samar da takin zamani a duniya.